Manchester United ta tuntuɓi Xavi kan maye gurbin Ten Hag, West Ham na zawarcin Terzic

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Barcelona Xavi ya tattauna da Manchester United kan yiwuwar maye gurbin Erik ten Hag a matsayin koci. (Mail)
Tsohon kocin Borussia Dortmund Edin Terzic na kan gaba cikin ƴan takarar neman muƙamin kocin West Ham idan Hammers ta kori Julen Lopetegui. (Florian Plettenberg)
Chelsea ta shaida wa dan wasan bayan Ingila Josh Acheampong mai shekaru 18 cewa ba zai sake buga wa kulob ɗin wasa ba har sai ya sanya hannu kan sabon kwantaragi. (Athletic)
Tottenham ta sanya farashin £80m kan ɗan wasan bayan Sifaniya Pedro Porro, mai shekara 25, wanda Manchester City ke zawarcinsa. (Football Insider)
Brighton da Arsenal na zawarcin golan Aston Villa ɗan ƙasar Poland Oliwier Zych mai shekara 21. (Telegraph)
Kocin Arsenal na ƴan kasa da shekara 18 Jack Wilshere, mai shekara 32, zai koma Norwich a matsayin kocin tawagar farko a wannan makon bayan ƙungiyoyin biyu sun amince kan diyyar da za a biya kan tsohon ɗan wasan tsakiya na Gunners. (Standard)
Graham Potter da David Moyes da kuma Gareth Southgate su ne za su iya maye gurbin Oliver Glasner idan Crystal Palace ta sallame shi. (Guardian)
Dortmund na son siyan dan wasan baya na gefen hagu a watan Janairu inda ta sanya ido kan da ɗan wasan Chelsea Ben Chilwell mai shekaru 27 da kuma ɗan kasar Hungary Milos Kerkez, mai shekara 20, na Bournemouth. (Teamtalk)
Manyan ƴan wasa a nahiyar Turai na iya kin tallata sabuwar gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi da aka faɗaɗa a wani ɓangare na takaddamar da ke tsakanin ƙungiyoyin ƴan wasa da Fifa kan jaddawalin wasannin ƙwallon ƙafa. (Times)










