Elon Musk na neman a tsige Trump daga mulki

Donald Trump da Elon Musk

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Babban attajirin na duniya wanda kuma a baya-bayan ya babe tsakaninshi da Shugaba Trump, bayan ya kasance kusa a gwamnatin - Elon Musk, ya tsaya kan matsayinsa na neman a tsige shugaban daga mulki.

Sai dai ya janye barazanar da ya yi ta ficewa daga wani muhimmin shirin Amurka na sararin samaniya.

Hamshakin attajirin ya sauya shawara ne 'yan sa'o'i bayan ya ce zai soke aikin kumbon zuwa sararin samaniya da ya yi wa lakabi da SpaceX Dragon.

Wannan rigima ta barke ne har ta kai aka ga tsofaffin shakikan biyu a rana – bayan hamshakin attajirin wanda mako daya baya yake zaman lamba daya da kusan ba kamarshi a gwamnatin ta Trump, bayan ya soki shugaban kasar kan sababbin dokokinsa kan haraji, da kuma kudurin dokar gwamnatin na kashe kudade.

Cikin wani saƙo da hamshaƙin attajirin ya wallafa a shafinsa na X, ya yi wa Trump gori da cewa ba don taimakonsa ba da Trump din ya fadi zaɓen shugaban ƙasar.

Bugu da kari ya goranta wa Shugaba Trump da cewa in ba don taimakon da ya bayar ba da tuni Trump din bai ci zabe ba, kuma jam'iyyar hamayya ta demokrats ce ke da rinjaye a majalisar dattawan ƙasar.

Mista Musk - wanda ajiye aikinsa a gwamnatin Trump a makon da ya gabata - ya zargi Shugaba Trump da rashin godiyar Allah.

Attajirin lamba daya na duniya ya kuma zargi shugaban kasar mafi karfi a duniya da kasancewar sunansa a takardun binciken sirri na abin kunya da ba a kai ga bayyanawa ba da ke da alaka da shahararren attajirin nan da aka samu da laifin lalata da kananan yara wato Jeffrey Epstein wanda ya hallaka kansa a gidan yari, kodayake Mista Musk bai bayar da wata sheda da ke tabbatar da ikirarin nasa ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai dai a martanin da shugaba Trump ya mayar ya ce Elon Musk ya ba shi kunya, yana mai cewa attajirin ya fara sukarsa ne bayan da ya yanke tallafin da ake bai wa ababen hawa masu amfani da lantarki.

Haka kuma Mr Trump, wanda kalaman na Musk suka tunzura ainin ya yi barazanar soke kwangilolin da gwamnatinsa ta kulla ko ta ba kamfanonin Mista Musk.

Wannan rikici tsakanin tsofaffin aminan biyu ta sa darajar hannun jarin kamfanin Mista Musk na mota mai amfani da lantarki , Tesla ta sulmuyo kasa da sama da kashi 14 cikin dari a Amurka.

An yi wannan rabuwa ta dutse a hannun riga ne tsakanin mutanen biyu – duk da cewa ma'aikatar da Trump ya bai wa Musk shugabanci ta inganta ayyukan gwamnati, ta kasance daya daga cikin wadanda suka fi fice a kwana darin farko na gwamnatin ta Trump – saboda yadda ta rufe hukumomin gwamnati da dama da korar dubban ma'aikata da sunan tsuke bakin aljihu.

Ba a dade ba aka fara rade-radin lokaci da kuma yadda jiga-jigan mutanen biyu za sur aba gari.

To amma kuma zuwa dan wani lokaci wannan rade-radi tamkar ya bi iska. A duk lokacin da ake ganin kamar lokacin rabuwarsu ya zo sai a ga kamar sun dinke barakar da ake gani ta kunno kai a tsakaninsu sun doshi gaba, Trump ya tsaya kai fata tare da Musk duk kuwa da yadda ake ganin babban mai ba shi shawarar na kara bakin jini tare da rikici da jami'an gwamnati, kuma yake zamar wa gwamnati bakar-kadara.