Trump ya bayar da umarnin sake bude kurkukun kare-kukanka da ke tsakiyar teku

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya umarci hukumomin gwamnatinsa da su sake budewa tare da fadada, tsohon gidan yari na Alcatraz, da ya yi kaurin suna, wanda ke wani tsuburi a California.
A wani sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta da muhawara na Truth Social, Trump ya ce tsawon lokaci manya kuma miyagun masu laifi da ke tuban-muzuru sun addabi Amurka.
Shugaban na Amurka ya ce ya umarci hukumar gidan yari tare da ma'aikatar shari'a da hukumar binciken manyan laifuka,, FBI da kuma hukumar kula da tsaron cikin gida da su yi aiki tare su sake bude wannan gidan yari da ya yi kaurin suna tare kuma da fadada shi, domin tsare wadanda Trump din ya kira kasurguman masu aikata laifi a Amurka.
Shugaban yana samun sabani da kotuna a kan manufarsa ta tura wadanda ake zargi da kasancewa 'yan kungiyoyin bata-gari zuwa gidan yari a kasar El Salvador.
A watan Maris da ya gabata ya aika da wani gungun 'yan daba sama da mutum 200 'yan kasar Venezuela El Salvador.
Haka kuma shugaban na maganar tura masu laifi 'yan kasar ta Amurka zuwa gidajen yari na kasashen waje.
A 1963 ne aka rufe gidan yarin, kuma a yanzu tsibirin na Alcatraz na zaman waje ne na ziyarar bude idanu.
Trump ya ce, Tunani ne kawai da na yi saboda alkalan yawancin wadannan alkalan masu tsatsatauran ra'ayi, suna son yi wa kowa ne daya sharia – ka duduba wannan abu – duk mutum daya da yake kasarmu ba tare da izini ba, da ya zo ta haramtacciyar hanya.
Hakan na nufin miliyoyin shari'o'i, wannan abin haushi ne.''
Wannan waje Alcatraz ya dade zaman alama ta doka da oda, kuma yana da wani tarihi, gaskiya. Saboda haka ina ganin za mu yi hakan, kuma muna duba abin a yanzu haka.''
Shi dai wannan gidan yari na Alcatraz da farko an gina wajen ne a matsayin wata hasumiya ta tsaro kuma aka sake gyara da gina shi a farkon karni na 20 a matsayin gidan yari na soji.
A shekarun 1930, ya koma karkashin ikon ma'aikatar sharia ta Amurka, inda ya zama gidan yari na tarayya – daga cikin kasurguman 'yandaba da miyagun masu laifi da aka tsare a gidan kason sun hada da Al Capone da Mickey Cohen da George ''Machine Gun '' Kelly.














