Ja-da-baya ko sake shiri: Me ya sa Trump ya janye haraji?

Asalin hoton, Getty Images
A kwanaki baya, Donald Trump da gwamnatinsa sun dage kai da fata cewa babu gudu babu ja da baya wajen lafta haraji kan gomman ƙasashe.
Har ma wasu daga cikin jami'an gwamnatin suke dariya a farkon lokacin da wani rahoto ya fito, wanda ke nuna cewa shugaban ƙasar ya amince da ɗaga ƙafa na kwana 90 kan ƙaƙaba harajin, wanda cikin ƙanƙanin lokaci ya sa kasuwar hannun jarin duniya ya samu tagomashi.
Amma yanzu da aka tabbatar da labarin ɗaga-ƙafar, yanzu ke nan cika alƙawarin da Trump ya yi na yin garambawul domin bunƙasa ɓangaren masana'antaun ƙasar Amurka zai ɗan samu tsaiko.
Fadar gwamnatin Amurka ta ce fito na fiton na farkon, kafin a ɗan tsagaita, dama tun farko an yi ne domin shiga tattaunawa da ɗaiɗaikun ƙasashe.
"Yanzu sama da ƙasashe 75 ne suke tuntuɓe mu, sannan na san wasu ma za su kawo kansu," in ji Scott Bessent, sakataren baitul malin ƙasar Amurka a tattaunawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan sanarwar.
Don haka shin janyewa ce Amurka ta yi saboda turjiya da fara fuskanta, ko kuma irin dabarar Trump ce kafin ya shiga tattauawa?
Jim kaɗan bayan sanarwar ne wasu daga cikin hadiman Trump - waɗanda da farko suka nuna cewa ba gudu ba ja da baya a farko - suka fito suna murnar sabon matakin gwamnatin ƙasar.
Mai ba shugaban ƙasar shawara kan cinikayya, Peter Navarro ya ce sabon sauyin ya zo a daidai lokacin da ya dace, kuma a yadda ya dace.
Babu cikakken bayani kan dakatar da harajin na Trump, wanda a shafinsa na sada zumunta na Truth ne ya sanar. Amma shin janywar har da ƙasashen tarayyar turai? domin sanya turan na nufin har da Mexico da Canada, waɗanda tun a farko sun yi watsi da kashi 10 ɗin da ya lafta. Shin harajin zai shafi wasu ɓangarori ne kawai?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da yammacin ranar Laraba, Trump ya tabbatar da cewa ana samun koma baya a harkokin kasuwancin duniya, kuma "mutane na nuna damuwarsu" bayan da farko ya fara nuna babu ruwansa da abin da ake faɗa.
Tun da farko ya bayyana a shafinsa na sadarwa na Truth, inda yake kira ga mutane da su "kwantar da hankalinsu," sannan ya yi alƙawarin cewa, "komai zai tafi yadda ya kamata."
A ƙarshe dai shi Trump ɗin ne da kansa ya jingine yunƙurin domin yin wasu gyare-gyare a tsarin nasa.
Ya nanata cewa sanarwar lafta harajojin lamari ne da bai yi da-na-sani ba, inda yake nuna cewa taɓarɓarewar tattalin arzikin lamari ne da aka yi sakaci da shi da daɗewa.
A nata ɓangaren, jam'iyyar Democrats ta nuna rashin dadinta kan matakan na Trump, inda shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa na ƙasar, Chuck Schumer ya zargi Trump da "gudanar da mulki mai cike da ruɗani."
Sai dai ana tunanin abubuwan da suka sa Trump ya ɗauki matakin nan na jingine yunƙurin wataƙaila ba su ba ne abubuwan lura.
Wannan matakin dai kamar yadda aka gani, ya sa kasuwar hannun jarin duniya ta ɗaga, amma sai dai yanzu kuma takun-saƙar kasuwanci tsakanin China da Amurka na ƙara zafi, kasancewar harajin da ya lafta wa China ya kai kashi 125.
Dole wannan matakin ya shafi harkokin kasuwancin duniya, amma dama hakan na cikin tsarin harkokin wajen Amurka - ko a mulkin tsohon shugaban ƙasar, Joe Biden wanda ɗan jam'iyyar Democrat ne haka lamarin yake - domin suna da sha'awar rage ƙarfin China.
Yanzu babban abin jira shi ne shin matakan da Trump ya ɗauka a makonnin baya - jefa ƙawayen Amurka cikin ruɗu da barazanar samar da sabuwar tsarin kasuwanci a duniya - za su yi wani tasiri.
Sannan kuma nan da kwana 90, bayan wannan matakin na jinginewar da Trump ya yi ta ƙare, wataƙaila diramar da aka shiga a wannan makon za ta iya sake komawa ɗanya jagab.











