Man City za ta sayar wa Barca Silva, Morata zai koma Atletico Madrid

Bernardo Silva

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Manchester City ta kulla yarjejeniya domin sayar da Bernardo Silva, dan wasan tsakiya mai shekara 27 ga Barcelona kan akalla fam miliyan 42. (Manchester Evening News)

Manchester United za ta mayar da hankalinta kan dauko Ismaila Sarr dan wasan gaba mai shekara 24 daga Watford. Wannan matakin ya biyo bayan janyewar da ta yi ne kan sayo Marko Arnautovic. (Sun)

Atletico Madrid ta yi wa United tayin sayen Alvaro Morata, dan wasan gaba mai shekara 29 wanda a baya ya taba buga wa Chelsea. (ESPN)

Dan wasan gaba na PSV Eindhoven Cody Gakpo mai shekara 23 na cikin 'yan wasan da Manchester United ke sha'awar sayowa amma za ta biya kimanin fam miliyan 35. (Telegraph - subscription)

Arsenal na tattunawa da AC Milan kan sayo Sandro Tonali, dan wasan tsakiya mai shekara 22, sai dai Milan na bukatar a biya ta fam miliyan 46. (Daily Mail) Kocin Arsenal Mikel Arteta na son kungiyarsa ta riga Liverpool dauko Yeremi Pino, dan wasan gefe na Villareal mai shekara 19 kan fam miliyan 33. (Metro) Chelsea na iya mika tayi mafi tsoka a tarihi kan Wesley Fofana, dan wasan tsakiya mai shekara 21 kuma dan kungiyar Leicester. (talkSPORT) Chelsean dai na sake kokarin mika tayi ga Inter Milan kan sayo Cesare Casadei dan wasan tsakiya mai shekara 19 kan fam miliyan 12. (Evening Standard) Sannan Chelsea za duba yiwuwar raba Pierre-Emerick Aubameyang, dan wasan gaba mai shekara 33 da kungiyarsa ta Barcelona domin ya koma Gasar Firimiya. (FourFourTwo) Barcelona ta shira mika wa Juventus Memphis Depay, dan wasan gaba mai shekara 28 kuma dan kasar Netherlands. Wannan matakin zai sa ta sami sauki kan matsin tattalin arziki da kungiyar ke fama da shi. (Goal)