Thiago Alcantara zai yi jinyar makonni da yawa a Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Dan kwallon Liverpool, Thiago Alcantara zai yi jinyar makonni da yawa, bayan da ya ji rauni ranar Asabar a wasan Premier League.
Dan kwallon tawagar Sifaniya, mai shekara 31, sai sauya shi aka yi a minti na 51 a wasan da suka tashi 2-2 a Fulham a Craven Cottage.
Za a sake auna girman raunin dan wasan a cikin makon nan, koda yake Liverpool na hangen raunin ba wani mai tayar da hankali bane.
'Yan wasan da ke jinya a Liverpool kawo yanzu sun hada da Curtis Jones da kuma Alex Oxlade-Chamberlain.
A cikin watan Agusta Liverpool za ta fafata da Crystal Palace da Manchester United da Bournemouth da kuma Newcastle, sannan ta ziyarci Everton ranar 3 ga watan Satumba a wasan hamayya.







