Watakil Varane ya yi bankwana da Man Utd, Matip na nazarin barin Liverpool

An wallafa

Manchester United na shirin bai watsohon dan wasan baya daga Faransa Raphael Varane, mai shekara 31, damar barin kungiyar idan kwantiragin da ya ke kai ya kare. (Mirror)

Barcelona na duba yiwuwar karfafa 'yan wasanta na gaba da zabin saye dan wasan Liverpool da Colombia, Luiz Dias mai shekara 27. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Dan wasan Kamaru Joel Matip, mai shekara 32, na cikin 'yan wasan da ake ganin zai iya barin Liverpool a wannan kaka yayin da yake samun tayi daga Roma da Lazio. (Corriere - in Italian)

Manchester United na shirin rabuwa da 'yan wasanta da dama a wannan kaka domin cimma dokokin kudi na hukumar wasanni, inda yanzu haka ta soma nazari kan makomar dan wasan Ingila, Marcus Rashford, mai shekara 26. (Express)

AC Milan na zawarcin dan wasan Aston Villa da Brazil Diego Carlos, mai shekara 31, bayan bajintar da ya nuna kwana nan. (Sport - via TeamTalk)

Dan wasan baya a Fulham Tosin Adarabioyo, mai shekara 26, ya shaidawa kungiyar cewa yana son tafiya a karshen kaka. Tuni ya soma samun tayi daga Liverpool da Tottenham da Newcastle. (Express)

Dan wasan Brighton da Japan Kaoru Mitoma, mai shekara 26 na janhankalin kungiyoyi irinsu Arsenal da Manchester City da Manchester United. (Fichajes - via 90min)

Paris St-Germain ta fuskanci babban komabaya a kokarin saye dan wasan Barcelona da Sifaniya Lamine Yamal, mai shekara 16. (AS - in Spanish)

Arsenal da Tottenham Hotspur sun shiga zawarcin dan wasan West Ham da Ingila mai buga tsakiya Daniel Rigge, dan shekara18. (ESPN)

Bayern Munich ta tabbatar cewa tana tattaunawa da tsohon kocin Manchester United Ralf Rangnick a kokarin maye gurbin Thomas Tuchel. (Goal)

Tsohon kocin Chelsea da Tottenham Antonio Conte ya cimma yarjejeniya shekara uku da Napoli.(Rai - in Italian)

Real Madrid ba zata cigaba da bibbiyar dan wasan Bayern Munich Alphonso Davies ba, mai shekara 23. (Relevo - in Spanish)

Arsenal ta soma tattauna kan dan wasan Brazil mai shekara 26, Gabriel Magalhaes, 26. (Mirror)

Barcelona ta gabatar da sabon kwantiragi na shekara biyar mai kwabi kan dan wasanta Pau Cubarsi, wanda Manchester City ke kwadayi. (AS - in Spanish)

Bologna na fatan tsawaita zaman kocinta Thiago Motta da ke samun tayi daga Juventus da Manchester United. (Gazzetta dello Sport, via Football Italia)