Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saura maki daya tsakanin Arsenal da Man City a Premier
Manchester City ta je ta doke Brighton 4-0 a kwantan wasan Premier League da suka kara ranar Alhamis.
Minti na 17 da fara tamaula City ta ci kwallo ta hannun Kevin de Bruyne daga baya Phil Foden ya kara biyu a raga - haka suka je hutu City na cin 3-0.
Kwallo biyun da Foden ya ci sun zama na 50 a Premier League, ya zama na uku matashi mai shekara 23 da ya zura 50 a babbar gasar tamaula karkashin Pep Guardiola, bayan Lionel Messi and Erling Haaland.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne City ta kara na hudu ta hannun Julian Alvarez, hakan ya sa ta hada maki ukun da take bukata.
Wannan shi ne karo na hudu a jere da Manchester City ta zura kwallo hudu a raga ko fiye da haka a Premier League, bayan kwazon Manchester United a Afirilun 2000.
Haka kuma City ta taba yin wannan bajintar a Mayun 2022 da kuma Arsenal, wadda ta yi hakan a Maris din kakar nan.
Arsenal ce ta daya da maki 77 a kan teburin Premier League, wadda ta sharara 5-0 a ragar Chelsea ranar Talata.
City ta koma ta biyu da maki 76, mai kwantan wasa, wadda ta kai wasan karshe a FA Cup, bayan da Real Madrid ta fitar da ita a Champions League na bana.
Liverpool, wadda ta lashe Carabao Cup a kakar nan, amma aka fitar da ita a FA Cup da Europa League tana ta ukun teburi da maki 74.
Ranar Laraba Liverpool ta ci karo da koma baya, sakamakon da Everton ta doke ta 2-0 a Goodison Park a wasan hamayya na Mersyside Derby.
Saura wasa hurhudu ya rage a gaban Arsenal da Liverpool, yayin da Manchester City mai rike da kofin bara take da biyar a gabanta.
Ranar Asabar 27 ga watan Afirilu Liverpool za ta je gidan West Ham United a wasan mako na 35 a Premier League.
Sai a ranar Lahadi 28 ga watan Afiri za a yi wasan hamayya tsakanin Tottenham da Arsenal da wanda Manchester City za ta ziyarci Nottingham Forest.
Wasannin mako na 35 a Premier League
Ranar Asabar 27 ga watan Afirilu
- West Ham United da Liverpool
- Fulham da Crystal Palace
- Manchester United da Burnley
- Newcastle United da Sheffield United
- Wolverhampton da Luton Town
- Everton da Brentford
- Aston Villa da Chelsea
Ranar Lahadi 28 ga watan Afirilu
- Tottenham da Arsenal Week
- Bournemouth da Brighton
- Nottingham Forest da Manchester City