Spain ta kafa kwamitin da zai kula da harkar kwallon kafar kasar

An wallafa

Gwamnatin Sifaniya ta kafa wani sabon kwamiti na musamman da zai kula da harkokin hukumar kwallon kafar kafar.

Kwamitin ne zai ci gaba da jan ragamar hukumar, har zuwa zaben shugaba, bayan takaddama da Luis Rubiales ta kai ya hakura da jagoranci.

An tsare Rubiales a farkon watan nan a wani zargi da ake yi masa kan cin hanci da rashawa.

Haka kuma ana sa gurfanar da shi a kotu kan zargin sunbatar 'yar wasa Jenni Hermoso a lebe a gasar kofin duniya, wadda ba ta amince da hakan ba.

Gwamnatin Sifaniya ta shiga sabgar, bayan da hukumar kwallon kafar ta fada rudani da zubar da mutuncin kasar a idon duniya a fannin tamaula.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa da ta Turai, Uefa sun ce suna ci gaba da sa ido, ba su ji dadin abinda ke faruwa ba.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta fayyace karara cewar za ake gudanar da hukumar kwallon kafar mambobinta mai cin gashin kai, ba tare da yin katsalanda ba.

Fifa da Uefa za su bukaci karin bayanai kan yadda za a gudanar da hukumar kwallon kafar kasar, idan bai ci karo da doka ba, kafin yin zaben.