Palace ta yi wa Eze da Olise farashin £60m kowanne

An wallafa

Crystal Palace ta dora farashin ga duk kungiyar da ke son sayen Eberechi Eze da wadda ke son daukar Michael Olise kan £60m ga kowanne dan wasan.

Palace ba ta fuskantar barazanar barin Premier League a kakar nan, wadda take kaka ta 12, wadda ba ta bukatar sayar da 'yan wasan da take da su.

To sai dai rawar da mai shekara 25, Eze ke takawa tare da mai shekara 22, Olise, ta kwan da sanin cewar kungiyoyi da dama za suyi zawarcin su da an kare kakar nan.

Saboda haka Palace ta ce sai kungiya ta tanadi £60m ga kowanne dan kwallon biyu, kafin ta amince a fara cinikin sayar da su.

A kakar nan Olise da Eze suka saka hannun kan kunshin kwantiragi mai tsawo da za su ci gaba da taka leda a Selhurst Park, kenan Palace ba ta da wata damuwa.

A kakar bara an yi ta rade-radin cewar Eze zai koma Manchester City, wadda daga baya ta sayi Matheus Nunes daga Wolves maimakonsa.

Haka kuma Chelsea ta kasa karasa cinikin Olise kan kudi £35m kan fara kakar nan.

Ranar Laraba Palace ta doke Newcastle United a kwantan Premier League mako na 29 a Selhurst Park.