Danbindiga ya harbe ma'aikatan jakadancin Isra'ila biyu a Amurka

Asalin hoton, Reuters
Wani dan bindiga ya hallaka wasu ma'aikatan ofishin jakadancin Isra'ila mace da namiji a babban birnin Amurka, Washington.
Danbindigan wanda ke tsare a yanzu, ya bude musu wuta ne a daidai lokacin da suke fitowa daga wajen wani taro da suka halarta a wani gidan adana kayan tarihi na Yahudawa.
Duk da cewa babu wassu cikakkun bayanai game da wannan hari, zuwa yanzu, to 'yansanda sun tabbatar da cewa mutumin da ake zargi da bude wa ma'aikatan biyu wuta, a daidai lokacin da suke fitowa daga dakin kayan tarihin na Yahudawa a Washington, yana hannu.
'Yansandan sun ce mutumin wanda sunansa Elias Rodriguez, mai shekara 30, ya rika furta kalaman 'yanci ga Falasdinawa a lokacin da aka kama shi.
Shugaban kungiyar Yahudawa da ke Amurka ya ce kungiyarsa na gudanar da wani taro ne a dakin adana kayana tarihin lokacin da aka kai harin.
Jakadan Isra'ila a Amurka ya ce wadanda aka harben matasa ne da suke shirin yin aure.
Hukumomi sun ce bayanai sun nuna daman an ga mutumin a kusa da wannan gini da abin ya faru – wanda yana daura da ofishin babbar lauyar gwamnatin Amurka, Jeanine Pirro wadda samun labarin abin da ya faru ke da wuya ta garzaya wajen domin gani da idonta abin da ya faru kamar yadda bayanai suka ce.
Jami'an tsaro sun ce babu wani bayani da suke da shi na zargin maharbin a baya.
Mai magana da yawun ofishin jakadancin Isra'ila a Washington Tal naim Cohen, ya rubuta a shafinsa na X, cewa danbindigan ya harbi mutanen ne a kusa da kusa, bayan sun fito daga wannan gini.
Ya ce suna da kwarin gwiwa a kan jami'an tsaro a dukkannin matakai wajen kare wakilai da alummar Isra'ila a duk fadin Amurka.
A sakon da ya sanya a shafinsa na sada zumunta da muhawara Shugaba Donald Trump ya yi Alla-wadarai da harin, yana mai nuna cewa an kai harin ne bisa tsana da kiyayya ta Yahudawa wadda ya ce dole ne a kawo karshen hakan yanzu.
Ya kuma mika ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen biyu da aka harbe.
Ya ce kiyayya da tsana tsattsaunran ra'ayi ba su da gurbi a Amurka.
Shugaban kasar Isra'ila Isaac Herzog da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio su ma dukkaninsu sun yi Alla-wadari da kisan na Yahudawan biyu.








