Ƴan sandan Ghana sun kama waɗanda ake zargi da kisan soja

Asalin hoton, Ghana Police Service
Ƴan sanda a Ghana sun kama mutum shida da ake zargi da kashe wani matashin soja mai suna Imoro Sheriff a unguwar Ashaiman.
An kama mutanen ne a wurare daban-daban inda suka ɓoye.
A cikin wata sanarwa da ƴan sanda suka fitar, sun ce sun kama waɗanda ake zargin ne a kwanaki daban-daban har zuwa 12 ga watan Maris.
Bayanin ya ƙara da cewa a ranar huɗu ga watan Maris, 2023 ne wasu matasa biyu suka far wa sojan a unguwar Taifa Ashaiman a wajen babban birnin ƙasar Accra, a yunƙurinsu na ƙwace wayarsa.
A lokacin da sojan ya turje musu sai suka soka masa wuƙa a hannu, sannan suka gudu da wayar tasa.
Hukumar sojojin ƙasar ta ce ta kama mutum 184 a unguwar ta Ashaiman, kankisan sojan.
An samu gawar sojan ne jina-jina sanadiyyar yankan da aka yi masa.
Rundunar sojin ta ce sojan ya fita daga bariki ne, bayan da ya samu izinin zuwa ganin mahaifansa.
A ranar Talatar makon da ya gabata ne sojoji suka dira a unguwar, inda aka zarge su da uzzura wa al’umma ta hanyar shiga gidajen mutane da yi ma wasu duka.
Sai dai daga baya hukumar sojin ta yi ƙarin haske kan lamarin, inda ta ce jami’anta sun je unguwar ne domin zaƙulo waɗanda ake zargi da kisan sojan.
Ƴan sanda sun ziyarci iyalin mamacin a ranar Lahadi domin yin ƙarin haske kan halin da ake ciki game da binciken da ake yi.
A ranar Litinin ake sa ran gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.









