Ghana ta nemi afuwa kan 'zaluncin' da ake zargin sojoji da aikatawa

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin ministan tsaron Ghana Kofi Amankwa-Manu ya nemi afuwar 'yan ƙasar sakamakon wuce-gona-da-iri da sojoji suka yi lokacin da suka je aiki a Ashaiman, wata unguwa da ke kusa da birnin Accra , ranar Talata domin kwantar da hankula.
An kai sojojin ne bayan da wasu mahara suka kashe wani matashin soja a garin sakamakon daɓa masa wuƙa da suka yi.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta yaɗa hotuna da bidiyon da ke nuna yadda sojojin ke muzgunawa al'umma a lokacin samamen nasu.
''In dai ta tabbata an muzguna wa mazauna Ashaiman waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, a wannan aiki da sojoji suka je yi, to a matsayina na mataimakin ministan tsaro, ina mai bayar da haƙuri game da haka'', in ji mista Amankwa-Manu, a wata tattaunawa da ya yi da wani gidan talabijin na ƙasar.
"Abu ne da ya kamata mu fito mu bayyana cewa a duk lokacin da aka samu kuskure lokacin wani aiki, to amma ba wai muna bayar da haƙuri ba ne kan aiwatar da samamen''.
Mista Amankwa-Manu ya ce rundunar sojin ƙasar ta dakatar da samamen ''domin gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata mummunan laifi''.
Wani ɗan majalisa daga yankin ya ce kusan mutum 72 aka kama a lokacin samamen sojojin.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Ghana ta ce an kai samamen ne domin zakulo masu laifi domin ɗaukan fansar kashe jami'inta da aka yi ba.
Sai dai sanarwar, wadda ta samu sa hannun daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Birgediya-Janar E. Aggrey-Quashie, ta ƙara da cewa rundunar ta yi takaicin yadda ayyukan sojojin ya tayar da hankulan wasu fararen hula a yankin.
Ta ku mua buƙaci al'umma da su taimaka mata wajen fallasa masu aikata laifuka.









