Dibling ya ɗauki hankalin Utd, Tottenham, Chelsea da PSG na son Gyokeres

Tyler Dibling

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Matashin ɗan gaban Southampton Tyler Dibling mai shekara 18 ya ɗauki hankalin Manchester United bayan da ya burge darektan wasanninta Dan Ashworth. (GiveMeSport)

Manchester United za ta gabatar wa matashin ɗan wasanta na tsakiya Kobbie Mainoo, na Ingila mai shekara19, sabon kwantiragi mai gwaɓi sosai da zai nuna sabon matsayinsa na kasancewa cikin tawagar farko ta masu buga wa ƙungiyar wasa. (Fabrizio Romano a YouTube)

Wataƙila Manchester United ta nemi ɗan wasan tsakiya na Bayern Munich Leon Goretzka, na Jamus mai shekara 29, saboda rashin tabbas kan makomar, Christian Eriksen da kuma Casemiro a ƙungiyar. (Manchester Evening News)

Tottenham da Chelsea da Paris St-Germain na kan gaba a ƙungiyoyin da ke son sayen ɗan gaban Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, daga Sporting ta Portugal. (Caught Offside)

Liverpool na duba yuwuwar sayen ɗan bayan Juventus da Brazil Gleison Bremer, mai shekara 27, a matsayin wanda zai iya maye gurbin Virgil van Dijk, mai shekara 33. (Teamtalk)

Newcastle na sa ido a kan matashin ɗan gaban Norway Sindre Walle Egeli, mai shekara 18, wanda ake yi wa laƙabi da magajin Erling Haaland, yayin da su ma ƙungiyoyin West Ham da Crystal Palace da Brighton da Brentford ke son matashin mai shekara 18, wanda aka yi masa kuɗi fam miliyan 25. (Daily Mail)

Ɗan bayan Bayer Leverkusen Jeremie Frimpong, na Holland mai shekara 23, na cikin jerin ƴan wasa biyar da Chelsea ta ware domin zaɓar wanda zai maye gurbin Reece James, mai shekara 24. (TBR Football)

To amma kuma Chelsean ba za ta bayar da aron matashin ɗan gaba na gefe na Brazil Estevao Willian mai shekara 17, idan ya koma ƙungiyar daga Palmeiras a bazara mai zuwa ba. (Goal)

Inter Milan na son sayen ɗan bayan Arsenal da Japan Takehiro Tomiyasu a watan Janairu, inda Gunners ɗin ke neman fam miliyan 25 a kan ɗan wasan mai shekara 25. (Daily Mirror)

Manchester City ta zaƙu ta fara tattaunawa a kan kwantiragin mai tsaron ragarta Ederson, mai shekara 31, kasancewar kwantiragin ɗan with the Brazil ɗin na yanzu zai ƙare a bazarar 2026. (TBR Football)

Ɗan wasan tsakiya na Newcastle Joelinton, na son yin ritaya daga ƙwallon ƙafa a ƙasarsa Brazil, to amma a yanzu dai zuciyarsa na nan daram Newcastle ɗin. (Chronicle)