An gurfanar da tsohon ɗan wasan Arsenal bisa zargin safarar ƙwaya

Asalin hoton, SNS
Ɗan wasan ƙwallon ƙafa Jay Emmanuel-Thomas ya gurfana a gaban kotu bayan an tuhume shi da kitsa yunƙurin safarar miyagun kwayoyi.
Ɗan wasan mai shekaru 33, wanda a halin yanzu yake taka leda a Greenock Morton, an kama shi ne a gidansa da ke Gourock, kusa da Glasgow, ranar Laraba kuma aka kai shi Carlisle don amsa tambayoyi.
Tsohon ɗan wasan na Arsenal bai amsa laifi kan tuhumar da ake masa a kotun Majistare ta Carlisle ba amma lauyansa ya ce ya musanta hannu a duk wani shiri na shigo da ƙwayoyi zuwa Birtaniya kuma yana so shari'ar ta gudana domin ya sami damar wanke kansa.
Gurfanar da ɗan wasan na zuwa ne bayan da jami’an hukumar yaƙi da manyan laifuka ta ƙasa (NCA) suka gano tabar wiwi mai nauyin kilogiram 60 da aka ƙiyasta kuɗinta ya kai fam 600,000 a cikin wasu akwatunan da suka isa filin jirgin saman Stansted daga Bangkok.
An tsare Emmanuel-Thomas a gidan yari bayan da aka ki amincewa da buƙatarsa ta neman beli.
Jay Emmanuel-Thomas tsohon ɗan wasan Ingila ne na ƴan ƙasa da shekara 17 da ƙasa da shekaru 19 wanda a baya ya taɓa bugawa ƙungiyoyi da suka haɗa da Livingston da Aberdeen da Ipswich town da Bristol City da Queens Park Rangers da Arsenal da Cardiff City da kuma kungiyar PTT Rayong ta Thailand.
Ɗan wasan na fuskantar hukuncin ɗaurin shekara 14 a gidan yari idan har aka same shi da laifi.






