Mount da Hojlund sun kusa dawowa taka leda a United

Mason Mount da Rasmus Hojlund

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An samu ƙarin labarin da zai sake kwantar wa magoya bayan Manchester United hankali bayan nasarar da suka samu a kan Barnsley da ci 7-0 a tsakiyar mako.

Mason Mount da Rasmus Hojlund duk sun dawo sun fara atisaye.

Kocin United Erik ten Hag ya bayyanawa manema labarai gabannin tafiyar United zuwa Crystal Palace a ƙarshen wannan makon, duk da dai bai yi bayani kan ko ƴan wasan za su iya shiga tawagar da za ta yi wasa a Selhurst Park ba.

Dukansu sun kasance suna fama da matsalolin cinya.

Mount ya sami rauni ne a wasa na biyu na gasar Premier a Brighton, yayin da shi kuma Hojlund ya sami rashin sa'a ne tun a wasan share fage da Arsenal a Los Angeles a watan Yuli.

United tana mataki na 10 a kan teburin premier na bana bayan ta ci wasa biyu ta kuma yi rashin nasara a guda biyu cikin wasanni huɗun da ta buga ya zuwa yanzu.