PSG na zawarcin Osimhen da Rashford,Liverpool na son Geuhi

An wallafa

Liverpool na sha’awar dan wasa mai tsaron baya na Crystal Palace da Ingila Marc Guehi dan an shekara 23 (Telegraph - subscription required)

Paris St-Germain na zawarcin dan wasa mai kai hari na Napoli da Nijeriya Victor Osimhen, mai shekara 25. da dan wasan gaban Manchester United da ingila Marcus Rashford mai shekara 26 da dan wasan tsakiya na Barcelona da Sfaniya Gavi dan shekara 19 a wannan bazara (The i)

Manchester United da Liverpool na cikin kungiyoyin firmiya league da ke son dan wasan tsakiya na Atalanta Ederson, kuma ita ma Arsenal da Newcastle da kuma Tottenham suma suna sha’awar dan wasan Brazil mai shekara 24. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Ita ma Juventus ta na son Ederson, sai dai kungiyar ta Serie A ta yanke shawarar dauko abokin wasansa a Atalanta Teun Koopmeiners dan shekara 25 dan wasan tsakiya na Netherlands (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Manchester United na zawarcin dan wasa mai tsaron baya na Juventus da Brazil Gleison Bremer mai shekara 26 akan euro miliyan 70 (Calciomercato - in Italian)

Mataimakin shugaban Fulham Tony Khan ya ce kungiyar za ta yi nazari akan tayin da ta ga dace da aka yi kan dan wasan tsakiya na Portugal Joao Palhinha mai shekara 28 (Talksport)

Manchester United na son ta sake zawarcin dan wasa mai kai hari na Bayern Munich da Ingila Harry Kane mai shekara 30 da dan wasan tsakiya na Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong dan shekara 26 a wannan bazara (Football Transfers)

Aston Villa ta soma Shirin siyan dan wasan tsakiya na Red Bull Salzburg Oscar Gloukh dan shekara 19 dan kasar Israila wanda kuma ke jan hankalin Manchester United da Arsenal da Liverpool da Newcastle United da kuma Barcelona inda an yi masa tayin euro miliyan 20 (Ekrem Konur)

Sheffield Wednesday da Bolton Wanderers da Peterborough United na duba yuwar daukar dan wasan tsakiya na Jamaica Ravel Morrison dan shekara 31 wanda ba shi da kungiyar da yake taka wa leda bayan ya bar kungiyar DC United a Amurka. (Teamtalk)