Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG na zawarcin Osimhen, Mbappe bai gamsu da tayin Real Madrid ba
Dan wasan gaba na Paris St-Germain Kylian Mbappe, mai shekara 25, da wakilansa ba su gamsu da sabon tayin da Real Madrid ta yi wa dan wasan Faransa a baya baya nan ba a kan cewa zai iya komawa wani kulob ba tare da shinge ba a wannan bazara, saboda tayin bai kai irin wanda suka yi masa a Watan Mayun 2022 ba . (Athletic - subscription required)
Tottenham na da kwarin gwiwar cewa kocinta Ange Postecoglou, mai shekara 58 ,zai ci gaba da aiki a kungiyar duk da cewa Liverpool na son daukarsa ya yi mata aiki yayin da ta ke neman wanda zai maye gurbin Jurgen Klopp a wannan bazara. (Telegraph - subscription required)
West Ham ta jinkirta tattaunawa da kocinta David Moyes, mai shekara 60, yayin da kungiyar ta maida hankali wajen kawo karshen rashin nasara a wasanni bakwai da ta buga a jere a duk gasa. (Mail)
Paris St-Germain na zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 29, inda zakarun tura su biya fam miliyan 51 a kan shi. (Fichajes - in Spanish)
Manchester United na son ta dauko dan wasan bayan Bayern Munich Matthijs de Ligt, mai shekara 24, yayin da dan wasan Netherlands din bai ji dadin rawar da ya taka a gasar zakarun Jamus ba . (Sun)
Ita ma Arsenal na ci gaba da zawarcin De Ligt amma Manchester United it ace a gaba . (Football Transfers)
Manchester United na kuma zawarcin wasu 'yan wasan baya na Bayer Leverkusen , inda kocin kungiyar Erik ten Hag ke son dauko dan wadan baya na gefe dama na Netherlands Jeremie Frimpong, mai shekara 23, da dan wasa baya na Burkina Faso Edmond Tapsoba, dan shekara 25. (Manchester Evening News)
Haka kuma Ten Hag ya nemi sayan dan wasa mai kai hari na Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, dan shekara 26. (Fichajes - in Spanish)
Arsenal da Liverpool duk suna sha’awar siyan dan wasan gefen Portugal Pedro Neto daga Wolves, wadanda ke son sayar da dan wasan dan shekara 23 a kudin da suka ga ya dace saboda matsin tattalin arzki. (Fichajes - in Spanish)
Chelsea na zawarcin dan wasan baya ta gefe hagu na Bournemouth da Hungary Milos Kerkez, dan shekara 20, tare da dan wasan baya na Bayern Munich da Canada Alphonso Davies, dan shekara 23. (Football Transfers)
Fulham ta gaza a wani yunkuri na sayan dan wasa mai kai hari na Borussia Dortmund Sebastien Haller a watan Janairu saboda dan wasan mai shekara 29 ya so ya maida hankali a kan gasar cin kofin Afirka tare da Ivory Coast kuma ba ya son ya sauya kulob a tsakiyar kakar wasa . (Fabrizio Romano)
Barcelona za ta cefanar da mai tsaron baya na Denmark Andreas Christensen, mai shekara 27, da dan wasan gefe na Brazil Raphinha, mai shekara 27, domin rage yawan kudin da take kashewa kan albashi . (Mirror)
Barcelona da Real Madrid da Liverpool na zawarcin Kocin Bayern Leverkusen Xabi Alonso . (Sport - in Spanish)
Paris St-Germain ta saka dan wasan gefe na AC Milan da Portugal Rafael Leao, dan shekara 24, da dan wasa mai hari na Napoli da Nigeria Victor Osimhen, mai shekara 25, a cikin jerin sunnayen wadanda ta ke son ta dauko idan Mbappe ya bar kungiyar a wannan bazara (La Repubblica - in Italian)
Dan wasa mai kai hari na Porto da Iran Mehdi Taremi, mai shekara 31 na gab da yin gwajin lafiyarsa ,a Inter Milan tare da komawa can a wannan bazara. (Fabrizio Romano)
Dan wasan tsakiya na Manchester United Kobbie Mainoo dan shekara 18 zai amince da duk wani kira na Ingila amma kuma yana son ya buga wa kasar Ghana wasa. (Mail)