Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mbappe zai koma Real Madrid a karshen kakar nan
Ɗan kwallon Paris St-Germain, Kylian Mbappe ya amince zai koma taka leda a Real Madrid idan an kammala kakar bana.
Ƙyaftin din tawagar Faransa, mai shekara 25 ya sanar da PSG cewar zai bar kungiyar da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen kakar watan Yuni.
Har yanzu Mbappe bai kai ga cimma yarjejeniya ba da Real Maadrid, amma ana sa ran kungiyar za ta sanar da halin da ake ciki nan gaba kadan.
Ɗan wasan PSG shi ne kan gaba a ci wa kungiyar kwallaye, inda yake da 244 a raga, wanda ya lashe kofin duniya a tawagar Faransa a Rasha a 2018.
Mbappe ya bukaci a fayyace makomarsa kafin cikin watan Maris, wanda ya tattauna da shugaban PSG, Nasser Al-Khelaifi ranar 13 ga watan Fabrairu da cewar yana son komawa Real Madrid.
Bayan da aka san cewar Mbappe na son barin kungiyar tun ranar Alhamis, hakan ya sa ba a fara saka shi ba a gasar Ligue 1 ranar Asabar a wasa da Nantes.
Daga baya ya shiga karawar, wanda ya ci ƙwallo a bugun fenariti, tuni PSG ta bayar da tazarar maki 14 a kan teburin Ligue 1.
An ce ana sa ran zai amince da kunshin yarjejeniyar kaka biyar da zai ke karbar £12.8m a kowacce kakar tamaula.
Haka kuma Real za ta bai wa Mbappe £128m kudin rattaba ƙwantiragi da ladan wasa da sauransu da za a biya cikin shekara tara - sannan zai ke karbar kashi na tallukansa.
Tuni kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya fara tunanin wurin da zai ke saka Mbappe tare da Jude Bellingham da kuma Vinicius Junior.
Idan kuma Luka Modric ya bar Real Madrid a karshen kakar bana, Mbappe ne zai karbi riga mai lamba 10, irin lambar da yake sa wa a PSG.