Napoli ta raba gari da Mazzarri ta kuma ɗauki Calzona

An wallafa

Napoli ta raba gari da kociyanta, Walter Mazzarri bayan wata uku yana kan aikin ta kuma maye gurbinsa da Francesco Calzona.

Mazzarri ya karbi aikin kociyan Napoli a hanun Rudy Garcia cikin watan Nuwamba ya kuma bar kungiyar tana ta tara a teburin Serie A.

Ɗan kasar Italiya, Calzona, mai shekara 55 ya yi aikin mataimaki karkashin Maurizio Sarri da kuma Luciano Spalletti.

Calzona zai ja ragamar tawagar Slovakia a gasar nahiyar Turai ta Euro 2024, wanda ya kulla yarjejeniya da Napoli zuwa karshen kakar bana.

Kociyan na da yarjejeniya da Slovakia zuwa karshen kakar 2025, wadda za a iya tsawaita masa ita da zarar tawagar ta samu gurbin shiga gasar kofin duniya a 2026.

Napoli, mai rike da kambun Serie A na bara za ta karbi bakuncin Barcelona a Champions League ranar Laraba.