Gaza 'nan gaba kaɗan za ta kasance babu man fetur, magunguna da abinci'
Zirin Gaza na daf da faɗawa cikin wata sabuwar matsalar ayyukan jin ƙan ɗan'adam idan aka hana kayan buƙatun rayuwa shiga yanki, a cewar hukumomi, yayin da Isra'ila ta mayar da martani ga hare-haren ƙungiyar Hamas.
Mazauna Zirin Gaza sun ce ba a shigar da kayan agaji ba tun ranar Asabar, kuma a ranar Litinin Isra'ila ta ayyana "datse komai gaba ɗaya" a yankin - inda ta ce za a yanke hasken lantarki da shigar da abinci da man fetur da kuma ruwan sha.
Gaza, yanki ne da mutane kimanin miliyan 2.3 ke rayuwa, kuma kashi 80 cikin 100 na mutanen sun dogara ne a kan kayan agaji.
Mutane sama da 500 ne suka mutu a can, yayin hare-haren ramuwar gayya na Isra'ila.
Isra'ila ce ke iko da sararin samaniyar Gaza da gaɓar ruwanta, kuma tana iyakance mutane da kayayyakin da za su iya tsallakawa cikin yankin..
Masar ita ma, tana matukar taƙaita mene ne da kuma wane ne zai tsallaka cikin Gaza, ta hanyar kan iyakarta da yankin.
Tun bayan hare-haren safiyar Asabar, Isra'ila ta dakatar da duk kayan masarufin da ke shiga Zirin Gaza, ciki har da abinci da magunguna. Mutane da dama a yanzu ba su da lantarki da intanet, kuma nan gaba kaɗan ba za su iya samun muhimman kayan buƙatun rayuwa, kamar abinci da ruwan sha ba.
Hukumomi sun yi gargaɗin cewa man fetur ɗin da ake da shi a Zirin Gaza, zai iya ƙarewa a cikin sa'a 24 zuwa 72.
Hukumar ayyukan jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargaɗin cewa man fetur ɗin da ake da shi ba zai wuce kwanaki ƙalilan ba.
Ko kafin taƙaita al'amura a baya-bayan nan, mazaunan Gaza tuni suke fama da tsananin ƙarancin abinci da taƙaita zirga-zirga da kuma ƙarancin ruwan sha.
A ranar Litinin, ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce za su ƙaƙaba wani matakin "datse komai gaba ɗaya" a yankin.
"Ba lantarki, babu ruwan sha, babu iskar gas - duka za a datse SU," in ji shi, ya ƙara da cewa "muna faɗa da dabbobi ne kuma za mu ɗauki mataki gwargwado."
Ministan samar da ababen more rayuwa na Isra'ila daga bisani ya ba da umarnin katse ruwan sha zuwa Gaza nan take, yana cewa: "Abin da aka saba yi a baya, ba za a yi shi ba a nan gaba."
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar lafiya ta al'ummar Falasɗinawa ta ce asibitoci na fuskantar ƙarancin magunguna da kayan amfanin asibiti da man fetur saboda matakan Isra'ila.
Ta yi kira ga ƙasashen duniya su buƙaci Isra'ila ta "dawo da hasken lantarki", kuma ta samar da muhimman buƙatun rayuwa kamar magunguna da man fetur da jannaretocin lantarki.

Asalin hoton, Reuters













