Jackson zai je Bayern Munich, Hojlund na nazari kan Napoli

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta amince da yarjejeniyar ba da aron ɗan wasanta na Senegal, mai shekara 24, Nicolas Jackson ga Bayern Munich. (Bild - in German)
Ɗan wasan tsakiya a Ingila, Kobbie Mainoo mai shekara 20, na nazarin barin Manchester United nan gaba kaɗan. (Talksport)
Crystal Palace ta gabatar da tayin fam miliyan 15 kan ɗan wasan Manchester City Manuel Akanji, mai shekara 30. (Sun)
Ɗan wasan gaba a Manchester United da Denmark Rasmus Hojlund mai shekara 22, zai samu karin albashi idan ya amince ya koma Napoli. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Tottenham za ta fuskanci kalubale a karo na huɗu a kokarin sayen ɗan wasan Como bayan watsi da tayin fam miliyan 50 da aka gabatar kan ɗan wasan na Argentina mai shekara 20, Nico Paz. (Mirror)
Wolves za ta gabatar da sabon kwantiragi kan Jorgen Strand Larsen bayan watsi da tayin fam miliyan 50 daga Newcastle, amma har yanzu akwai kwaɗayin cefanar da shi idan har za a ba ta fam miliyan 75. (Telegraph - subscription required)
Strand Larsen na matukar son zuwa Newcastle amma ba a masa kallon wanda zai maye gurbin Alexander Isak mai shekara 25, da Liverpool ke farauta. (The I - subscription required)
Jami'ai a Newcastle har da ɗaya daga cikin masu ƙungiyar, Jamie Reuben, sun tuntubi Isak a kokarin shawo kansa duk da farautar Liverpool. (Daily Mail)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kocin Wolves Vitor Pereira na son ɗauko ɗan wasan Girona, Ladislav Krejci mai shekara 26. (Guardian)
Borussia Dortmund na gab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan Wolves mai shekara 23, Fabio Silva. (, externalAthletic - subscription required)
Ɗan wasan Everton da Scotland Nathan Patterson ya ɗau hankalin Sevilla da ke son ɗaukansa aro. (Liverpool Echo)
West Ham ta yi watsi da tayin Everton kan ɗan wasanta na tsakiya mai shekara 30 daga Czech, Tomas Soucek. (Times - subscription required)
Mai buga tsakiya a Brazil Andreas Pereira mai shekara 29, na da damar barin Fulham a wannan kakar. (Teamtalk)
Daraktan Roma zai tattauna da Liverpool kan ɗan wasan Girka, Kostas Tsimikas mai shekara 29, wanda Marseille ke nuna kwaɗayinta. (Football Italia)
Crystal Palace ta shiga farautar ɗan wasan Toulouse da Faransa, Jaydee Canvot mai shekara 19. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasan tsakiya a Bournemouth Philip Billing mai shekara 29, zai koma Denmark domin ci gaba da taka leda a Midtjylland kan yarjejeniyar fam miliyan 5. (Times - subscription required)








