Arsenal na zawarcin Eze, Man Utd ta ƙulla yarjejeniyar sayen Mbeumo

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal a shirye take ta tunkari Crystal Palace domin tattauna ko za su iya ƙulla yarjejeniya kan ɗanwasan Ingila Eberechi Eze ba tare da taɓo batun kuɗin sakinsa na fam miliyan 68 ba. (Talksport)
Liverpool ta tattauna da ɗanwasan Crystal Palace Jean-Philippe Mateta mai shekara 28 inda ɗanwasan na ƙasar Faransa ya gana da wakilan ƙungiyar a Paris. (Footmercato - in French)
Manchester United ta cimma yarjejeniya da Brentford kan ɗanwasan Kamaru Bryan Mbeumo mai shekara 25. (Football Transfers)
Brentford na duba yiwuwar ɗauko ɗanwasan Ipswich Town da Ingila na ƴan ƙasa da shekara 21 Omari Hutchinson mai shekara 21 a matsayin wanda wataƙila zai maye gurbin Mbuemo. (Standard)
Wakilin Joao Felix ya sa baki a ƙoƙarin ganin an daidaita kan yarjejeniyar komawar ɗanwasan gaban na Chelsea zuwa Benfica. (A Bola - in Portuguese)
Bayan yin tattaunawar farko a watan Janairu, Chelsea na ci gaba na nuna sha'awar sayen ɗanwasan Manchester United mai shekara 21 wato Alejandro Garnacho. (TBR Football)
An alaƙanta ɗanwasan Faransa Benoit Badiashile mai shekara 24 da Marseille sai dai ya ce zai ci gaba da zama a Chelsea a kaka mai zuwa. (Footmercato - in French)
West Ham ta ƙara ƴan wasan Liverpool da ke taka leda a matakin ƴan ƙasa da shekara 21 Harvey Elliott da Tyler Morton cikin jerin ƴanwasan da take zawarci. (Mail)
Manchester United ta tuntuɓi Lyon don ta ji ko akwai damar sayen ɗanwasanta na ƙasar Faransa Corentin Tolisso. (L'Equipe - in French)
Ɗanwasan Gabon kuma tsohon mai bugawa Arsenal ƙwallo Pierre-Emerick Aubameyang mai shekara 36 ya shirya yin bankwana da Al-Qadsiah ta Saudiyya don komawa Marseille na Faransa. (La Provence - in French)
Manchester City za ta cefanar da ɗanwasan tsakiya na Ingila a matakin ƴan ƙasa da shekara 21 James McAtee mai shekara 22 a wannan bazara. (Football Insider)
McAtee ya isa Jamus domin ganawa da Eintracht Frankfurt a matsayin sabon kulob ɗin da wataƙila zai koma. (Fabrizio Romano)
Wolves ta kusa ƙulla yarjejeniyar fam miliyan 15 kan ɗanwasan Fluminense Jhon Arias mai shekara 27. (Mail)
Ɗanwasan tsakiya na Switzerland Granit Xhaka ya amince ya koma Neom SC ta Saudiyya wadda ba ta kai ga daidaitawa da Bayer Leverkusen kan farashin ɗanwasan mai shekara 32 ba. (Sky Sports Germany)












