Ƙarin harajin Trump ya zama mataki mafi rashin tabbas da ya ɗauka zuwa yanzu

Shugaban Amurka Donald Trump.

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Anthony Zurcher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Arewacin Amurka
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Tsarin siyasar Donald Trump ya sauya ainun a tsawon lokaci da ya ɗauka ana damawa da shi. Amma abu ɗaya da ya tsaya a kai tun 1980 shi ne, imanin da ya yi cewa samun haraji shi ne hanyar da ta fi dacewa wajen bunƙasa tattalin arzikin Amurka.

Yanzu yana amfani da damarsa ta shugaban ƙasa wajen ɗabbaƙa hakan.

A wani biki da ya gudanar a fadarsa ta White House tare da abokansa da ƴan siyasa masu ra'ayin riƙau da kuma muƙarraban gwamnatinsa, Trump ya sanar da ƙaƙaba sabbin haraje-haraje kan ƙasashe da dama - da ƙawayen ƙasar da sauransu.

A jawabin da ya yi, shugaban ya tuna da irin goyon bayan da ya daɗe yana yi kan haraji, da kuma sukar da ya yi tun farko a kan yarjejeniyoyin cinikayya mara shinge kamar Nafta da Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya.

Shugaban ya amince da cewa zai fuskanci suka a cikin kwanaki masu zuwa daga "faɗin duniya" da masu "buƙatu na musamman", amma ya buƙaci Amurkawa su amince da manufofinsa.

"Kada ku manta, duk wani hasashe da abokan hamayyarmu suka yi game da kasuwanci a cikin shekaru 30 da suka gabata an tabbatar ba daidai ba ne," in ji shi.

Yanzu, a wa'adi na biyu da yake ƙewaye da mashawarta da ra'ayinsu ya zo ɗaya, kuma su ke da rinjaye a jam'iyyar Republican da ke iko da majalisun dokokin ƙasar biyu, Trump na iya mayar da hangen nesansa na sabuwar manufar kasuwancin Amurka zuwa matabbaciya.

Waɗannan manufofin, in ji shi, sun sanya Amurka ta zama ƙasa mai arziki fiye da shekara 100 da suka wuce.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Shekaru da dama, an tilasta wa 'yan Amurka masu aiki tukuru su zauna a gefe yayin da suke ganin sauran ƙasashe na yin arziki da samun ƙarfi ta sanadiyyarsu," in ji shi. "Matakin na yau, zai sa mu samu damar sake mayar da Amurka ƙasa mai ƙarfi - mafi girma fiye da kowane lokaci."

Ana dai ganin matakin da Trump ya ɗauka na ƙaƙaba sabbin haraje-harajen na da haɗarin gaske.

Masana tattalin arziki sun yi gargaɗin cewa waɗannan manyan haraji - kashi 53 kan China da kashi 20 kan Tarayyar Turai da Koriya ta Kudu, tare da kashi 10 da aka saka wa wasu ƙasashe - za su kai kan Amurkawa, abin da zai janyo tashin farashi da barazanar koma-bayan tattalin arziki a duniya.

Ken Roggoff, tsohon babban masanin tattalin arziki a Asusun Ba da Lamuni na Duniya, ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar Amurka ƙasa mafi girman tattalin arziki a duniya ta faɗa cikin koma bayan tattalin arziki, kuma kashi 50 ya nuna za a iya samun haka bayan wannan sanarwar.

"Kawai ya jefa ruɗani a tsarin kasuwancin duniya," kamar yadda Mista Roggoff ya faɗa wa BBC, inda ya ƙara da cewa sakamakon da wannan matakin haraji kan kayayyakin da za a shigar Amurka ba zai yi kyau ba.

Shugaban Amurka Donald Trump.

Asalin hoton, Shutterstock

Matakin Trump zai iya kuma janyo barazanar ɓarkewar rikicin kasuwanci da sauran ƙasashe da kuma ƙawayen Amurka da tayi watsi da su - waɗanda take ƙoƙarin gyara alaƙar yanzu.

Alal misali, Amurka na ganin Japan da Koriya ta Kudu a matsayin masu bai wa China kariya wajen karfafa kasuwancinta. Sai dai a baya-bayan waɗannan ƙasashe sun sanar da cewa za su yi aiki tare don martani ga tsare-tsaren kasuwancin Amurka.

Amma, idan Trump ya samu nasara kan manufofinsa, zai sauya tsarin kasuwancin Amurka a duniya wanda ta taimaka wajen kikiro wa tun bayan yaƙin duniya na II.

Ya yi alkawarin cewa matakinsa zai sake inganta masana'antun Amurka da samar da sabbin hanyoyin samun kuɗin shiga da kuma saka ƙasar ta ƙara dogaro da kanta da kare kanta daga tsare-tsaren cinikayyar kayayyaki a duniya da suka janyo mata matsala lokacin annobar Korona.

Lamari ne mai wuya - wanda kuma mutane da dama ke ganin bai dace a yi ba. Sai dai ga shugaban da ke koƙarin assasa iƙonsa, ko da ta hanyar yaƙi, sauyawa wurare suna, samun sabbin yankuna ko kuma dakatar da shirye-shiryen gwamnati da ma'aikatanta, wannan ita ce nasarar da yake ganin ya dace a samu.

Ya yi wa ranar da take "ranar ƴanci".

Abin da ya fito ƙarara shi ne, sanarwar ta ranar Laraba wadda idan aka bi ta, za ta zama sabon babi a tarihi. Tambayar ita ce ko hakan zai zama nasara a tarihi ko kuma wadda za a san mutum kan abu mara kyau da ya aikata.

Jawabin Trump yana a matsayin babban nasara - wanda ya shafe irin tasiri mara kyau da lamarin zai haifar kan tattalin arzikin Amurka da kuma siyasarsa.

Sai dai, ya ce abin da ya yi abu ne mai kyau - duk da cewa a karshen jawabinsa an ga kamar shakku a fadar shugaban ƙasar.

"Lamarin zai kasance ranar da - za ku waiwaya a shekaru masu zuwa sannan ku ce, mun sani, yana da gaskiya."