Makomar; Paqueta, Musiala, Edwards, Adarabioyo, Wan-Bissaka, Gallagher

An wallafa

Da alama Manchester City na son Lucas Paqueta, saboda ya na son barin kungiyar West Hama a kakar wasan nan - amma sai idan an kammala binciken da hukumar kwallon kafa ke yi kan zargin karya dokar caca da ake yi wa dan wasan tsakiyar na Brazil mai shekara 26. (Guardian)

City na shirin kashe fam miliyan 120 domin sayo dan wasan tsakiya na Jamus mai taka leda a Bayern Munich Jamal Musiala mai shekara 21. (TeamTalk)

Liverpool na shirin dauko dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Sporting Lisbon Marcus Edwards, mai shekara 25, da mai tsaron gida na Portugal Goncalo Inacio, 22. (Football Insider)

Dan wasan gaba na Paraguay Miguel Almiron, mai shekara 30, da mai kai hari na Ingila Callum Wilson, 32, na daga cikin 'yan wasan da watakil za ku bar Newcastle United a daidai lokacin da kulub din ke shirin sauya 'yan wasa a kaka mai zuwa. (Telegraph - subscription required)

Manchester United da Tottenham na son dan wasan tsakiya na Ingila, mai bugawa kungiyar Fulham wasa Tosin Adarabioyo a kokarinsu na ganin an cimma matsaya kafin ainahin tattaunawa kan kwantiragin daukar dan wasan mai shekara 26. (TeamTalk)

Ana son saida dan wasan United Aaron Wan-Bissaka kan fam miliyan 13 ga Milan sakamakon mai tsaron baya na Ingilar dan shekara 26 ba shi da wani kwantiragi a kasa har zuwa shekarar 2025. (Gazetta dello Sport - in Italian)

Tottenham na kokarin ganin yadda za su yi saurin sasantawa kan dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Chelsea Conor Gallagher, dan shekara 24, da zarar an bude kasuwar 'yan wasa. (Sun)

Mai tsaron baya na Barcelona Pau Cubarsi na son sabon kwantiragi da Nou Camp, duk da kungiyoyi da dama na Turai na nuna sha'awar daukar matashin dan wasan mai shekara 17, tun bayan bajintar da ya nuna a wasansu da Paris St-Germain. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Arsenal da Liverpool sun bi takwararsu Bayern Munich a son dauko dan wasan gefe na Sifaniya Alejandro Grimaldo, mai shekara 28, daga Bayer Leverkusen. (Football Transfers)