Barcelona na neman Amorim, Arsenal na gwada sa'a a kan Kimmich

An wallafa

Barcelona na ƙoƙarin cimma yarjejeniya da kocin Sporting Lisbon, Ruben Amorim domin maye gurbin Xavi da ke bankwana, yayin da Liverpool da Bayern Munich ke sake nazarin zaɓinsu bayan Xabi Alonso ya yanke shawarar tafiya Bayer Leverkusen. (Independent)

Sai dai manyan shugabanni a Barcelona na ƙoƙarin ganin sun shawo kan Xavi ya ci gaba da zama da su. (Athletic)

Arsenal ta tuntuɓi Bayern Munich a kan ɗan wasanta na Jamus mai buga tsakiya, Joshua Kimmich, amma an faɗa musu cewa su jira sabuwar kaka. (Football Transfers)

Arsenal ta kuma nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan Real Sociedad mai shekara 25, Martin Zubimendi, da ake cewa watakil ya tafi Bayern Munich. (Caught Offside)

Manchester City da Liverpool na ganin ƙoƙarinsu na sayo ɗan wasan Bayer Leverkusen da Jamus, Florian Wirtz, mai shekara 20, na iya zama tarnaƙi idan Xabi Alonso ya ci gaba da zama a ƙungiyar ta Bundesliga. (HITC)

Manchester United na bibbiyar ɗan wasan Everton mai shekara 21, Jarrad Brathwaite da mai taka leda a Boca Juniors Aaron Anselmino mai shekara 18, da ɗan wasan Senegal Mikayil Faye a ƙoƙarin inganta tsaron bayansu a sabuwar kaka. (Mail)

Jadon Sancho da ke zaman aro a Borussia Dortmund, na iya sake samun dama a Manchester United, idan ƙungiyar ta ɗauko Jason Wilcox na Southampton a matsayin babban jami'in harkokin wasanni. (Manchester Evening News)

Manchester United na son ɗauko kocin Ipswich Kieran McKenna. Mutumin mai shekara 37 daga yankin Ireland ya yi aikin taimaka wa Jose Mourinho da Ole Gunnar Solskjaer a ƙungiyar. (Football Insider)

Real Madrid za ta sayo ɗan wasan baya a Lille, Leny Yoro mai shekara 18 da ake alaƙantawa da Manchester United da Liverpool da Chelsea. (Athletic)

Tottenham za ta fuskanci yanayi na dole ta sayar da ɗan wasanta na Brazil, Emerson Royal, mai shekara 25. (Football Insider)

Mai bugawa Leeds United da Ingila Archie Gray, ɗan shekara 18, ya shiga ran Real Madrid da Bayern Munich da wasu jiga-jigan ƙungiyoyin firimiya. (HITC)

Ɗan wasan Barcelona da Sifaniya Marcos Alonso na tattaunawa da Atletico Madrid. (Cadena Ser)

Barcelona na zawarcin ɗan wasan Fiorentina da Italiya, Michael Kayode, haka ma Arsenal. (Football Transfers)