Barcelona da PSG da 'yan Premier na son Messinho, Liverpool ta karkata ga Amorim

An wallafa

Barcelona na kara kaimi wajen ganin ta sayi matashin dan wasan gaba na gefe na Palmeiras, Estevao Willian wanda ake wa lakabi da Messinho, mai shekara 16 amma kuma Manchester City, da Manchester United, da Chelsea, da Arsenal da kuma Paris St-Germain su ma suna so dan Brazil din. (Mundo Deportivo)

Liverpool ta karkata ga kociyan Sporting Lisbon Ruben Amorim domin maye gurbin Jurgen Klopp bayan da Xabi Alonso ya ce zai ci gaba da zama a Bayer Leverkusen. (Liverpool Echo)

Amorim, mai shekara 39, yana da yarjejeniyar sayensa a kan fam miliyan 12.8 a kwantiraginsa. (Telegraph)

Ita ma Bayern Munich, wadda take son Alonso, dan Sifaniya a yanzu ta mayar da hankalinta kan kociyan Austria Ralf Rangnick, mai shekara 65, wanda a baya ya yi kociyan rikon kwarya a Manchester United. (Kicker )

Haka kuma Bayern din na son kociyan Brighton Roberto de Zerbi da kuma kociyan tawagar Jamus Julian Nagelsmann, wanda zakarun na Bundesliga suka kora shekarar da ta gabata. (Florian Plettenberg)

Graham Potter kuwa shi ne zai karbi aikin Borussia Dortmund shekara daya bayan sallamarsa da Chelsea ta yi. (HITC Football)

Real Madrid na sa ido a kan dan bayan Liverpool da Ingila Trent Alexander-Arnold kasancewar dan wasan mai shekara 25 ya tunkaro wata 12 na karshen kwantiraginsa a Anfield. (90min)

Liverpool na sha’awar danwasan gab ana gefe na Eintracht Frankfurt da Masar Omar Marmoush, mai shekara 25, ko da Mohamed Salah, mai shekara 31,zai bar Anfield a bazaran nan. (Mundo Deportivo)

Bisa ga dukkan alamu sai Barcelona ta tashi tsaye domin rike Joao Cancelo, wanda Manchester City, ta ba ta aro. Barca na son ta sake karbarsa aro to amma City kuma tana son ta sayar da shi kuma kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya tana sonshi. (Sport )

Watakila Manchester United ta nemi sayen dan bayan Juventus Gleison Bremer, dan Brazil mai shekara 27, wanda kwantiraginsa ya tanadi sayensa a kan yuro miliyan 60. (Repubblica - in Italian)

Za a sayar da dan wasan tsakiya na Belgium Amadou Onana, mai shekara 22, a bazaran nan a kan kudi mai yawa idan har Everton ta fadi daga gasar Premier. (Football Insider)

Tottenham ta shirya karbar tayi a kan danwasanta na tsakiya Pierre-Emile Hojbjerg, dan Denmark a bazaran nan. (Football Insider)

Aston Villa da Brighton na sha’awar sayen danwasan gaba na gefe na Leeds United Crysencio Summerville, na Holland a bazaran nan. (Football Insider)