Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
United da Spurs na son Summerville, Chelsea na harin Costa da Cambiaso
Manchester United da Tottenham na ci gaba da yunƙuri wajen ganin sun siyo ɗan wasan Netherlands Crysencio Summerville, daga West Ham. (Teamtalk)
Chelsea na sa ido kan mai tsaron ragar Porto Diogo Costa inda suke sa ran siyar da ɗan wasan kan fam miliyan 51. (Mirror)
Har ila yau Chelsea na harin ɗan wasan bayan Italiya Andrea Cambiaso, daga Juventus, sannan za su iya bayar da ɗan wasan Senengal Nicolas Jackson, a wani ɓangare na siyesa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Real Madrid na harin ɗan wasan Atlentico Madrid da Arjantina Julian Alvarez, a wani tayi da bai kankama ba, inda ɗan wasan na Bayern Munich Michael Olise ke kan gaba cikin jerin ƴan wasan da za su ɗauka, sannan Real Madrid ɗin na sa ran samun nasarar ɗaukar sa. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Manchester United ba su da wani shirin shiga sabuwar yarjejniya da Barcelona kan ci gaba da zaman Marcus RashFord a matsayin ɗan wasan aro a ƙungiyar. (ESPN)
Tottenham sun ƙi amince wa da tayin da Brighton ta yi a karo na biyu kan ɗan wasan Croatia Luka Vuskovic, da ya shafe kakar bara a matsayin ɗan wasan aro a Hamburg. (Sky Sports)
Tottenham sun fara tattunawa kan ɗan wasan Jamus Said El Mala daga Cologne, da fatan yin galaba kan Newcastle da Nottingham Forest, wajen siyen ɗan wasan. (Teamtalk)
Lazio da Feyenoord na sa ido kan makomar ɗan wasan Manchester City, Charlie Gary. (Football Insider)
Gotham FC sun amince da yarjejinya tsakanin su da ƴar wasan Australiya Sam Kerr, da ke shirin barin ƙungiyar mata ta Chelsea da ke buga gasar super League. (ESPN)