Newcastle na fargabar cefanar da Guimaraes, Leicester na farautar Nketiah

An wallafa

Newcastle United na fargabar dole ta bukaci sayar da dan wasanta na Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 26, domin cika ka'idar dokokin firimiya. PSG ta Faransa na kan gaba wajen farautarsa haka ma kungiyoyin Manchester United da Arsenal. (Sun)

Tottenham ta bi sahun Arsenal a farautar ɗan wasan Sweden, Alexander Isak, mai shekara 24, daga Newcastle. (Football Insider)

Sai dai Isak ya jadadda burinsa na cigaba da zama da Newcastle duk da tayin da yake samu daga kungiyotin firimiya. (inews)

Newcastle za ta bada fifiko wajen sayen 'yan wasan baya a kakar wasanni bayan rasa 'yan wasanta biyu Sven Botman da Jamaal Lascelles, da ke jinya. (Football Insider)

Ɗan wasan gaba a Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 25, na cikin jeren mutanen da Arsenal ke duba yiwuwar sayo wa, amma Sporting Lisbon na neman fam miliyan 85.6 kan duk mai son dan wasan. (Caught Offside)

Ɗan wasan tsakiya a Ingila, Kalvin Phillips mai shekara 28, zai fuskanci zabtarewar albashi idan ya kawo karshen zamansa a Manchester City ya koma Leeds United. (Mirror)

West Ham ba ta yarda ta tsawaita zaman aron Phillips ba a kungiyar. (Football Insider)

Manchester United na tattaunawa da ɗan wasan Nice mai shekara 23, Melvin Bard. (Evening Standard)

Mai bugawa Wolves tsakiya Max Kilman na cikin 'yan wasan na Manchester United ke hari a sabuwar kaka. (Times - subscription required)

Leicester City ta shiga farautar ɗan wasan Arsenal mai shekara 24, Eddie Nketiah, sai dai tana fuskantar kalubale daga Crystal Palace da Brentford. (Football Transfers)

Arsenal da Liverpool da Manchester United na cikin kungiyoyin firimiya da ke zawarcin ɗan wasan Bayer Leverkusen, Jeremie Frimpong. Dan kasar Netherlands mai shekara 23, ana neman fam miliyan 35 a kansa. (Football Insider)

Newcastle na bibbiyar ɗan wasan Real Madrid Dani Ceballos, mai shekara 27. (Mundo Deportivo - in Spanish)