'Yan Real Madrid da za su kara da Shakhtar a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta karbi bakuncin Shakhtar Donetsk a wasa na uku a cikin rukuni a Champions League da za su kara ranar Laraba a Sifaniya.
Real Madrid mai maki shida, mai rike da kofin tana ta daya a kan teburin rukuni na shida, bayan doke Cetik 3-0 da cin RB Leipzig 2-0.
Ita kuwa Shakhtar ta fara da cin RB Leipzig 4-1 a Jamus da yin 1-1 da Celtic tana ta biyu a rukuni mai maki hudu.
Sakamakon wasa da aka yi tsakanin kungiyoyin a gasar Zakarun Turai:
Real Madrid da Shakhtar Donetsk
2021/2022
Champions League Laraba 3 ga watan Nuwamba 2021
- Real Madrid 2 - 1 Shakhtar
Champions League Talata 19 ga watan Oktoban 2021
- Shakhtar 0 - 5 Real Madrid
2020/2021
Champions League Talata 1 ga watan Oktoban 2020
- Shakhtar 2 - 0 Real Madrid
Champions League Laraba 21 ga watan Oktoban 2020
- Real Madrid 2 - 3 Shakhtar
2015/2016
Champions League Laraba 25 ga watan Nuwambar 2015
- Shakhtar 3 - 4 Real Madrid
Champions League Alhamis 15 ga watan Satumbar 2015
- Real Madrid 4 - 0 Shakhtar
Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan Real Madrid da za su karbi bakuncin kungiyar Ukraine a Santiago Bernabéu. 'Yan wasan Real Madrid: Masu tsaron raga: Lunin, Luis López, Cañizares.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger, F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Lucas V., Tchouameni.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.









