'Yan Real Madrid da za su kara da Shakhtar a Champions League

An wallafa

Real Madrid za ta karbi bakuncin Shakhtar Donetsk a wasa na uku a cikin rukuni a Champions League da za su kara ranar Laraba a Sifaniya.

Real Madrid mai maki shida, mai rike da kofin tana ta daya a kan teburin rukuni na shida, bayan doke Cetik 3-0 da cin RB Leipzig 2-0.

Ita kuwa Shakhtar ta fara da cin RB Leipzig 4-1 a Jamus da yin 1-1 da Celtic tana ta biyu a rukuni mai maki hudu.

Sakamakon wasa da aka yi tsakanin kungiyoyin a gasar Zakarun Turai:

Real Madrid da Shakhtar Donetsk

2021/2022

Champions League Laraba 3 ga watan Nuwamba 2021

  • Real Madrid  2 - 1 Shakhtar     

Champions League Talata 19 ga watan Oktoban 2021

  • Shakhtar       0 - 5 Real Madrid

2020/2021

Champions League Talata 1 ga watan Oktoban 2020  

  • Shakhtar       2 - 0 Real Madrid

Champions League Laraba 21 ga watan Oktoban 2020

  • Real Madrid  2 - 3 Shakhtar     

2015/2016

Champions League Laraba 25 ga watan Nuwambar 2015

  • Shakhtar       3 - 4 Real Madrid

Champions League Alhamis 15 ga watan Satumbar 2015   

  • Real Madrid  4 - 0 Shakhtar  

Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan Real Madrid da za su karbi bakuncin kungiyar Ukraine a Santiago Bernabéu. 'Yan wasan Real Madrid: Masu tsaron raga: Lunin, Luis López, Cañizares. 

Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger, F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Lucas V., Tchouameni. 

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.