Man Utd na son Felix, PSG za ta rike Messi, 'yan Saudiyya na gogayya kan Ronaldo

An wallafa

Atletico Madrid za ta iya sayar da Joao Felix a kan yuro miliyan 100 bayan da ta sayi dan gaban na Portugal a kan yuro miliyan 126 a 2019.

Manchester United na sha’awar sayen dan wasan a watan Janairu amma kuma tana fuskantar gogayya daga daga Paris St-Germain da Bayern Munich.

Haka kuma PSG za ta gabatar wa Lionel Messi, tayin tsawaita kwantiraginta da shi bayan gasar Kofin Duniya.

Al Hilal na son doke abokiyar hamayyarta ta Saudiyya Al-Nassr wajen daukar Cristiano Ronaldo, bayan da ya raba gari da Manchester United. 

Chelsea na ci gaba da tattaunawa kan cinikin dan bayan RB Leipzig Josko Gvardiol kuma dan kasar ta Crotia ya ce watakila wata rana ta tabbata ya kasance a can.

Ita kuwa Atletico Madrid ta yi bincike ne a kan dan bayan Leicester Caglar Soyuncu, dan Turkiyya.

Manajan darektan Borussia Dortmund Carsten Cramer ya ce suna da kyakkyawar alaka da tsohon kociyan kungiyar kuma na Liverpool a yanzu Jurgen Klopp, amma ya ce ba za su sassauta ba idan har kungiyar ta Anfield na bukatar matashin dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19. 

Shi kuwa dan wasan tsakiya na Ingila Declan Rice, ya nuna cewa yana bukatar barin West Ham, inda ya ce yana son cin kofuna kuma ya taka leda a gasar Zakarun Turai.

Nottingham Forest ta cimma yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiya na Brazil Gustavo Scarpa, daga Palmeiras. 

Chelsea na gogayya da Newcastle United wajen sayen matashin dan wasan tsakiya na Brazil Andrey Santos, mai shekara 18, daga Vasco da Gama.

 

Dan wasan da Barcelona ta saya a bazara Franck Kessie bay a jin dadin zama a kungiyar, wadda ita ma ke duba yuwuwar sayar da dan tsakiyar na Ivory Coast ko da a kan yuro miliyan 10 ne.

Barcelonar na sha’awar sayen matashin dan wasan tsakiya na Brazil Endrick, mai shekara 16, amma kuma ba za ta gabatar da bukatarta ba kan dan wasan na Palmeiras a kakar nan ba.

Liverpool ta tattauna kan soke yarjejeniyar aron da ta bayar da Billy Koumetio tsawon kaka daya da Austria Vienna kasancewar kungiyar ba ta sa dan bayan dan Faransa mai shekara 20 a wasa sosai.