Qatar 2022: Morocco ta tsallake amma an fitar da Belgium

An wallafa

Morocco ta kai zagayen gaba a gasar kofin duniya da ake yi a Qatar, yayin da a ka cire Belgium bayan da ta kasa karbar maki uku hannun Croatia.

Nasarar da Morocco ta yi 2-1 a wasanta da Canada na nufin ta zama zakara a rukunin F da maki bakwai, yayin da Crotia ke binta da maki biyar.

Kasar ta Arewacin Afrika ta ci kwallayenta ne ta hannun Hakim Ziyech da En-Nesyri tun kafin a je hutun rabin lokaci.

Kuma ta zama kasa ta biyu daga nahiyar Afrika bayan Senegal da ta kai zagayen kwaf daya na Qatar 2022.

Belgium kuwa wadda ita ce ta biyu a jadawalin kwarewa na kasashen FIFA, kuma ta uku a gasar kofin duniya ta 2018, ta fita daga gasar da maki hudu.

Duk da Belgium tafi Croatia wadda ta buga wasan karshe a 2018 buga wasa mai kyau da kuma samun damarmaki, hakan bai sa ta samu maki ukun da take matukar bukata ba.

A yanzu Morocco da Croatia za su jira su ga wadanda za su kara da su a rukunin E, wanda ya kunshi kasashen Sfaniya da Jamus da Costa Rica da kuma Japan.

Kasashen na rukunin E za su take wasa ne da karfe takwas agogon Najeriya.