'Muna son ƴan Najeriya su taimaka su bankaɗo inda aka boye kuɗin sata'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon hirar
An wallafa

Shugaban hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa a Najeriya, Abdurrashid Bawa ya bukaci ƴan ƙasar da su taimaka wa hukumar gano inda wasu jami'ai ɓata-gari suka ɓoye kuɗaɗen gwamnatin da suka sace.

Ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da BBC Hausa, inda ya kuma nemi hadin gwiwar ƴan Najeriya a yaƙin da hukumar da yake jagoranta na shekaru biyun da suka gabata.