Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Muna son ƴan Najeriya su taimaka su bankaɗo inda aka boye kuɗin sata'
An wallafa
Shugaban hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa a Najeriya, Abdurrashid Bawa ya bukaci ƴan ƙasar da su taimaka wa hukumar gano inda wasu jami'ai ɓata-gari suka ɓoye kuɗaɗen gwamnatin da suka sace.
Ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da BBC Hausa, inda ya kuma nemi hadin gwiwar ƴan Najeriya a yaƙin da hukumar da yake jagoranta na shekaru biyun da suka gabata.