Sterling ya amince zai koma Chelsea daga Manchester City

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan wasan Manchester City, Raheem Sterling ya amince da kunshin yarjejeniyar da Chelsea ta gabatar masa, domin ya koma Stamford Bridge.

Mai shekara 27 yana da sauran kaka daya kwantiraginsa ya kare a Etihad, wanda kungiyoyi da dama ke zawarcinsa.

City ta dauki dan wasan daga Liverpool kan fam miliyan 49 a 2015, wanda ya ci wa City kwallo 131 a karawa 339 da ya yi mata.

Idan aka kammala cinikin, Sterling wanda ya buga wa tawagar Ingila wasa 77, zai zama na farko da Chelsea ta saya, tun bayan da wasu attajirai suka mallaki kungiyar karkashin Todd Boehly a bana.