Waiwaye: Ƙara wa shugaban ƙasa da 'yan siyasa albashi, sake fasalin takardun naira

Asalin hoton, State House
Hukumar tarawa da rarraba kudin haraji ta ƙasa ta ce ta kammala shiri domin sake duba albashin masu riƙe da muƙaman siyasa, da ma'aikatan shari'a, domin dacewa da halin da ƙasar ke ciki.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce a yanzu ana aiki ne da dokar da aka tsara tun shekarar 2008, wadda ta yi la'akari da yanayin da ake ciki lokacin da aka tsara dokar.
Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Engr. Elias Mbam na cewa za su sake duba albashin zaɓaɓɓun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa
Najeriya ta 'gargaɗi' Amurka kan barazanar tsaro

Asalin hoton, State House
Gwamnatin Najeriya ta nuna ɓacin ranta game da jerin gargaɗin da ofishin jakadancin Amurkar a Najeriya ke fitarwa kan barazanar kai hare-hare a wasu sasan ƙasar, har ma da Abuja.
A martanin da ta mayar ta bakin ministan yaɗa labaru Lai Mohammed, gwamnatin Najeriya ta ce mazauna Abuja da ma sauran yankunan ƙasar ba sa cikin haɗari.
Lai Mohammed ya ce “Ina tabbatar wa al’ummar Najeriya da na ƙasashen waje da suke zaune a Najeriya cewa jam’ian tsaro na bakin ƙoƙarinsu kan matsalar tsaro”.Ya ƙara da cewa “babu wata barazana, kuma babu baƙatar wani ya tayar da hankalinsa.”
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shawarci hukumomin tsaron ƙasar da dukkan al’umma da su ci gaba da yin taka tsantsan da kula kan sha’anin tsaro, amma kuma ya ce yana da matuƙar muhimmanci a guji tayar da hankula.
A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, shugaban ya nemi ƴan ƙasar da su kwantar da hankali. “Sabbin matakan barin ƙasar da Amurka da Birtaniya ke ɗauka ba za su zama dalilan tayar da hankali ba.
NNPC zai fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna

Asalin hoton, NNPC
Gwamnatin Najeriya ta amince ta ƙulla yarjejeniya da wani kamfani a Koriya ta Kudu da zimmar gyara matatar man fetur ta Kaduna da ke arewacin ƙasar.
Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kyari, shi ne ya saka hannu a madadin Najeriya yayin taro kan harkokin lafiya da tawagar ƙasar ke halarta a Koriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.
Sanarwar da NNPC ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce nan gaba kaɗan za a fara zagayen duba gyaran da za a yi.
INEC ta soke rajistar zaɓe miliyan uku

Asalin hoton, INEC
Hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya ta ce kashi 40 cikin 100 na sabbin waɗanda ta yi wa rajistar katin jefa ƙuri'a ɗalibai ne, tana mai cewa ta soke rajista kusan miliyan uku da suka saɓa wa ƙai'dojin hukumar.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya ƙara da cewa kashi 76 cikin 100 na masu zaɓe a ƙasar matasa ne.
A cewarsa yayin wani taro da jam'iyyun siyasa a Abuja ranar Laraba, an samu ƙarin masu katin jefa ƙuri'a 9,518,188 a kan 84,004,084 da ake da su, kuma a yanzu rajistar farko-farko ta nuna cewa jimillar adadinsu ya kai 93,522,272.
Babban bankin Najeriya zai sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankin zai sauya fasalin wasu takardun kuɗin kasar guda uku.
Ya ce babban bankin ya samu amincewar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari domin sauya fasalin takartun kuɗi na N200, da N500, da kuma takardar kuɗi ta N1000.
Babban bankin ya kuma umarci al’ummar ƙasar da su mayar da tsoffin kuɗaɗen da za a sauya zuwa banki.
CBN, ya ce idan mutane suka mayar da kuɗaden ba tare da ɓata lokaci ba, to za su iya samun musayar kudinsu a kan kari.









