Man Utd za ta yi sabon zubi, ko Haaland zai bar City?

Erling Haaland

Asalin hoton, PA Media

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Sabon kocin Manchester United Ruben Amorim na son ɗauko ɗanwasan da Algeria mai shekara 23, Rayan Ait-Nouri. (Sun)

Red Devils kuma na son ɗanwasan gaba na Chelsea Christopher Nkunku amma tana fuskantar hamayya daga Borussia Dortmund kan ɗanwasan na Faransa mai shekara 27. (Teamtalk)

Newcastle na son ɗanwasan gaba na Bournemouth da Ghana mai shekara 24 Antoine Semenyo amma ba za ta iya yin cefane ba har sai wasu ƴanwasan sun tafi. (Sky Sports)

Fulham da Leicester na sa ido kan ɗanwasan gaba na Brighton mai shekara 20 Evan Ferguson domin karɓar aronsa. (Football Insider)

Kocin Everton Sean Dyche ya samu cikakken goyon bayan mai ƙungiyar Farhad Moshiri kuma zai ci gaba da jan ragamar ƙungiyar. (Sky Sports)

Manchester United ta nuna sha'awarta kan matashin ɗanwasan Sporting mai shekara 17 Geovany Quenda na Portugal, wanda darajarsa ta kai fam miliyan 60. (A Bola - in Portuguese)

Red Devils kuma na son yin sabon zubin sabbin ƴanwasan gaba kuma cikin waɗanda take hari sun haɗa da ɗanwasan PSG da Faransa mai shekara 25 Randal Kolo Muani da ɗanwasan Eintracht Frankfurt da Masar Omar Marmoush, mai shekara 25. (Sky Germany - in German)

United kuma na sa ido kan ɗanwasan gaba na Wolves da Brazil mai shekara 25 Matheus Cunha, yayin da Tottenham ita ma ta nuna sha'awarta. (TBR Football)

AC Milan za ta shiga hamayya da Newcastle kan ɗanwasan gaba na Everton da Ingila mai shekara 27 Dominic Calvert-Lewin, yayin da Real Madrid ke son ɗauko ɗanwasan baya na ƙungiyar Jarrad Branthwaite, mai shekara 22. (Teamtalk)

Manchester City na da tabbacin ɗanwasanta na gaba Erling Haaland, mai shekara 24, zai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya kamar kocinsa Pep Guardiola. (Give Me Sport)

Barcelona na shirin lale fam miliyan 70 ga Sporting Lisbon kan ɗanwasan gaba na Sweden mai shekara 26 Viktor Gyokeres. (Sport - in Spanish)

Ɗanwasan baya na PSG mai shekara 29 Milan Skriniar na shirin komawa Juventus a Janairu. (Foot Mercato - in French)

Tottenham za ta shiga neman gola a Janairu bayan raunin da Guglielmo Vicario, mai shekara 28, ya samu a idon ƙafarsa. (Telegraph - subscription required)