Man Utd na son Quenda, Neymar zai koma Santos

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na ƙoƙarin cimma yarjejeniya kan matashin ɗan wasan Portugal mai shekara 17 Geovany Quenda. (A Bola - in Portuguese)
An shaida wa Manchester United cewa Sporting ba ta da wani zaɓi illa ta sayar da ɗan wasan gaba na Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, amma da wahala ta iya ɗauko shi a Janairu. (Mirror)
Barcelona na nazarin sabunta kwangilar mai tsaron raga Wojciech Szczesny makwanni bayan ya koma ƙungiyar. (Marca - in Spanish)
Kocin Aston Villa Unai Emery na iya sayar da ɗan wasan baya na Brazil mai shekara 31 Diego Carlos a Janairu. (Football Insider, external)
Ɗan wasan gaba na Brazil Neymar na shirin kowama tsohuwar ƙungiyar shi, Santos yayin da ƙungiyarsa ta Saudiyya Al-Hilal ta nuna rashin jin daɗi kan yawan raunin da ɗan wasan mai shekara 32 yake samu. (Cesar Luis Merlo)
Ɗan wasan tsakiya na Benfica da Turkiya Orkun Kokcu, mai shekara 23, ya jinjina wa kocin Liverpool Arne Slot yayin da ake hasashen ɗan wasan zai koma taka leda Anfield. (Liverpool Echo)
Fulham na shiga cikin masu hamayya kan ɗan wasan Brazil Igor Jesus daga Botafogo. (TBR Football)
Tottenham Hotspur na duba yiyuwar sake ɗauko ɗan wasan Ingila na tsakiya Harry Winks, mai shekara 28, bayan sayar da shi ga Leicester a bara. (Fichajes - in Spanish)
Arsenal na sa ido kan ɗan wasan gaba na Serbia mai shekara 24 Dusan Vlahovic da ke taka leda a Juventus. (Rudy Galetti)
Crystal Palace na son ɗauko ɗan wasan gaba a Janairu amma kuma ba ta da isassun kuɗi. (GiveMeSport)
Ɗan wasan Georgia Khvicha Kvaratskhelia, mai shekara 23, zai iya barin Napoli bayan kasa cimma matsaya yayin da Barcelona da Paris St-Germain ke farautarsa. (Goal)
Babu wani tsari ga Paul Pogba ya yi atisaye a Manchester United bayan ɗanwasan mai shekara 31 ya raba gari da Juventus. (Talksport)
West Ham da Southampton na hammaya kan tagwaye Cole da Dylan Williams da ke taka leda a Airdrie. (Sun)










