Ko Messi zai halarci bikin Ronaldo?

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo na shirin auren abokiyar zamansa Georgina Rodríguez bayan kusan shekara goma da suka shafe tare.
An ce an yi wa Ronaldo da Georgina baiko kwanan nan, bayan shekaru ana ta hasashen yaushe ne za su yi aure.
Ma'auratan sun shafe kusan shekara goma tare kuma suna da 'ya'ya tare.
A baya Ronaldo ya taɓa cewa zai yi aurensa ne bayan gasar cin kofin duniya, domin yana fatan ya lashe kofin kafin ya yi aure. Sai dai hakan bai samu ba.
Jaridar The Sun ta ruwaito cewa Ronaldo, wanda yanzu yake dab da yin ritaya daga buga ƙwallo, zai gudanar da gagarumin bikin aure a mako mai zuwa.
Rahotanni sun ce za a yi bikin a garin Funchal da ke tsibirin Madeira na ƙasar Portugal, inda aka haifi Ronaldo.
An kuma ce za a ɗaura auren ne a babban cocin Cathedral Church da ke Funchal.
Me zai hana Messi halarta?
Ana sa ran shahararrun mutane daga sassa daban-daban na duniya, kafafen yaɗa labarai da manyan attajirai za su halarci bikin.
Har yanzu ba a fitar da jerin sunayen waɗanda aka gayyata ba. Haka kuma ba a sani ba ko Lionel Messi, wanda ya daɗe yana gogayya da Ronaldo kan kambun Ballon d'Or, yana cikin waɗanda aka gayyata.
Abin lura shi ne Ronaldo bai halarci bikin auren Messi ba.
Daga baya kafafen yaɗa labarai ciki har da The Sun sun ruwaito cewa an kulle otal ɗin alfarma na Savoy Palace domin bikin, kuma za a rufe shi na tsawon kwana biyu daga ranar Asabar mai zuwa.
Rahotanni sun kuma ce Ronaldo mai shekara 41 da Georgina mai shekara 32 sun riga sun yi aure a asirce a bara.
Wace ce Georgina Rodríguez?

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan rabuwar Cristiano Ronaldo da tsohuwar budurwarsa, Irina Shayk, Georgina Rodríguez ta zama abokiyar rayuwarsa, lamarin da ya ja hankalin duniya.
Ronaldo ya taɓa bayyana a wata hira da Piers Morgan cewa yana matuƙar son Georgina kuma yana son su yi rayuwa tare har ƙarshen rayuwarsu.
A wani bikin ranar haihuwarta, ya haskaka wasu manyan gine-gine a Dubai da hotunanta domin nuna irin ƙaunar da yake mata.
Kafin Georgina, Ronaldo ya shafe shekara biyar yana soyayya da fitacciyar kwararriyar mai tallan kayan sawa ta Rasha, Irina Shayk.
Lokacin da aka sanar da rabuwarsu a 2015, 'yar'uwar Ronaldo, Elma, ta ce "Komai ƙaddara ne daga Allah."
Mutane da dama sun fassara wannan a matsayin cewa babu yiwuwar su sake komawa tare.
Ana kuma cewa Ronaldo ba ya da halin komawa ga macen da ya taɓa rabuwa da ita.
Haka kuma an ce baya son zama da macen da ba ta girmama mahaifiyarsa.
Bayanai kan Rodríguez
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mutane da yawa sun dade suna tambayar ko wace ce Georgina. A wani shiri game da rayuwarta, ta ce mafi yawan mutane sun san sunanta amma ba su san ainihin ko wace ce ita ba.
Georgina Rodríguez abokiyar rayuwar Cristiano Ronaldo ce, mai tallan kayan sawa, tsohuwar mai rawa kuma fitacciyar mai tasiri a kafafen sada zumunta.
Tana da sama da mabiya miliyan 44 a Instagram.
Ko da yake tana da takardar zama 'yar Spain, an haifi Georgina ne a Buenos Aires na Argentina.
Daga baya ta taso a birnin Jaca da ke arewacin Spain.
Jaca na da tazarar kusan kilomita 450 daga Madrid, kuma ƙaramin gari ne kusa da iyakar Faransa mai yawan jama'a kusan 13,000.
A lokacin tana aiki a matsayin ma'aikaciyar kula da baƙi.
Jaridar wasanni ta AS ta ce Ronaldo da Georgina sun haɗu ne a wani shagon Gucci da ke Madrid.
A lokacin Georgina tana aiki a matsayin mai tallace-tallace a shagon, yayin da Ronaldo ke taka leda a Real Madrid.
A cikin shirin rayuwarta, Georgina ta ce:
"Tsarinsa, jikinsa da kyawunsa sun ja hankalina nan take. Zan iya cewa na ƙaunace shi tun daga lokacin. Amma ni mutum ce mai kunya sosai."
Ta ƙara da cewa:
"Saboda kunyata, ya yi mini wuya in yi magana da wanda na haɗu da shi sau ɗaya kacal. Amma soyayya da kulawar da Ronaldo ya nuna mini sun canja komai."
Yadda Ronaldo ya nuna wa Rodríguez ƙauna
A lokacin Georgina tana zuwa aiki ne da motar haya saboda ba ta da mota, kuma wani lokaci ba ta da kuɗin sufuri.
Bayan Ronaldo ya san hakan, ana cewa yakan kai ta aiki da motocinsa masu tsada, lamarin da ke sa tsoffin abokan aikinta su fito waje domin kallon motocin.
Ba da jimawa ba, dangantakarsu ta bayyana ga jama'a, kuma masu ɗaukar hoto suka fara bibiyar su.
A shekarar 2016 ma an ga Ronaldo yana sanya gashin ƙarya da tabarau domin ka da mutane su gane shi.
Ana yaba wa Georgina saboda kulawar da take bai wa 'ya'yan Ronaldo. Tana da kyakkyawar alaƙa da babban ɗansa, Cristiano Jr., kuma ana yawan ganinta tare da shi a filayen wasanni suna kallon wasannin Ronaldo.
Mutane da yawa na ganin girmamawa da ƙaunar da take nuna wa iyali ne ya sa Ronaldo ke matuƙar daraja ta.
An haifi Cristiano Jr. a Amurka a shekarar 2010, amma har yanzu ba a bayyana ko wace ce mahaifiyarsa ta haihuwa ba.
Ronaldo ya ɓoye wannan sirri, yayin da mahaifiyarsa Dolores da Georgina suka taka muhimmiyar rawa wajen kula da ɗan nasa.











