Shin Portugal ta fi ƙoƙari a wasa idan babu Ronaldo - ko zai iya zaman benci?

Asalin hoton, Getty Images
An fara muhawara kan rawar da Ronaldo zai taka gabanin Kofin Duniya 2026.
Cristiano Ronaldo zai shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasa a tarihin ƙwallon ƙafa, amma wannan karo yana fuskantar tambayoyi da suka fi kowanne lokaci yawa game da matsayin sa a tawagar Portugal.
Wasan sada zumunta da Portugal ta buga da Kazakhstan a ranar 20 ga Agustan 2003 babu wani abin tunawa na musamman ga mutane da yawa. An buga fafatawar ne a ƙaramin filin mai ɗaukar mutum 8,000 kacal a birnin Chaves, kuma har sai da aka yi wa ciyawar filin fenti domin ta yi kyau. Sai dai wannan rana ta zama tarihi saboda ita ce ranar da Ronaldo ya fara taka leda a babbar tawagar Portugal.
A lokacin babu wanda zai yi tunanin cewa matashin ɗan wasan daga Madeira zai buga Kofin Duniya har sau shida. Amma yanzu, bayan shekaru sama da 20, Ronaldo mai shekara 41 yana shirin zama ɗaya daga cikin ƴan wasa kaɗan da suka taka leda a gasar sau shida, tare da Lionel Messi da Guillermo Ochoa.
Ronaldo shi ne kan gaba a tarihin cin ƙwallaye a matakin ƙasashe mai 143 a raga, kuma tasirinsa ya canza yadda Portugal ke kallon kanta a duniyar a fagen taka leda.
Joao Aroso, wanda ya yi aiki tare da Ronaldo tun lokacin da yake Sporting Lisbon har zuwa tawagar ƙasa, ya ce tauraron ya ba Portugal wata kima ta musamman a duniya.
"Mu ƙaramar ƙasa ce wadda ba kasafai take samun tasiri a duniya ba face ta hanyar ƙwallon ƙafa. Ronaldo ya taimaka wajen sa duniya ta san Portugal saboda kyawawan abubuwan da yake wakilta," in ji Aroso.
Sai dai duk da wannan tarihin, yanzu ana ci gaba da tattauna ko Ronaldo ya kamata ya ci gaba da kasancewa a sahun farko a Portugal.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsohon tauraron Portugal Antonio Simoes ya bayyana cewa Ronaldo yanzu yana ƙoƙarin kasancewa fitaccen mutum a fili fiye da taimaka wa tawagar wajen lashe kowanne kofin ne.
A nasa ɓangaren, kocin Portugal Roberto Martinez ya yi watsi da irin waɗannan maganganu, yana mai cewa alkaluman Ronaldo har yanzu suna nuna muhimmancinsa.
Martinez ya jaddada cewa Ronaldo ya ci ƙwallaye 25 cikin wasa 31 da ya buga wa Portugal tun lokacin da ya karɓi ragamar horar da ƙasar a 2023.
"Mun san muna magana ne kan ɗaya daga cikin mafiya girma a tarihin ƙwallon ƙafa. Yana cikin tawagar ne saboda har yanzu yana taka leda a mataki mai girma, ba saboda abin da ya yi a baya ba," in ji Martinez.
Duk da haka, masu sharhi na ci gaba da nuna cewa Portugal ta samu wasu manyan nasarori ba tare da Ronaldo ba. Tawagar ta doke Luxembourg da ci 9-0 a shekarar 2023 sannan ta lallasa Armenia 9-1 a bara, duk lokacin da Ronaldo bai buga ba.
Wannan ya sake tayar da tambayar ko Portugal na taka rawar gani idan ba tare da kyaftin ɗin nata ba.
Duk da waɗannan muhawarori, babu shakka Ronaldo zai kasance babban abin kallo da bibiya a Kofin Duniya a 2026. Ya ci ƙwallaye a kowace gasar Kofin Duniya guda biyar da ya buga a baya, kuma yana da ƙwallaye takwas a tarihin gasar jimilla, ƙwallo ɗaya kacal kasa da tarihin Portugal da Eusebio ya kafa.
Babban burinsa yanzu shi ne ya jagoranci Portugal zuwa ɗaukar kofin duniya na farko a tarihinta kafin ya yi bankwana da gasar mafi girma a duniya.
Idan har wannan ne Kofin Duniya na ƙarshe a rayuwarsa, Ronaldo zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa ya bar wata alama da ba za a manta da ita ba a tarihin ƙwallon ƙafa.
Ko Portugal ta fi taka leda duk lokacin da Ronaldo bai yi mata wasa ba?

Asalin hoton, Getty Images
Ronaldo ya riga ya tabbatar da cewa Kofin Duniya na 2026 zai kasance na ƙarshe a rayuwarsa da zai buga gasar.
Ko da yake ba ya kan ganiya shekaru sun ja, babu shakka Portugal za ta ci gaba da dogaro da shi yayin da za ta fara fatan neman lashe kofin duniya da wasa da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) a ranar 17 ga watan Yuni.
Tsohon ɗan wasan Portugal, Abel Xavier, ya shaida wa BBC World Service cewa:
"Cristiano ya fi yawancin ƴan wasan ƙwallo kafar kasae fahimtar manyan lokuta masu muhimmanci a wasa.
Wannan ƙwarewar ka iya zama abin da zai kawo bambanci a Kofin Duniya.
Kasancewarsa a cikin tawagar yana da matuƙar muhimmanci. Mutane suna mai da hankali ne kan basirarsa da ƙwazonsa, amma akwai bangaren fasaha da kuma tunani. Matasan ƴan wasa suna kallonsa a matsayin abin koyi kuma koyaushe yana bayar da wani abu mai amfani ga tawagar."
Tsohon mai tsaron ragar Portugal, Ricardo Pereira, wanda ya kasance a filin wasa lokacin da Ronaldo ya fara bugawa ƙasarsa wasa a 2003 kuma yanzu yana cikin masu horar da tawagar, ya bayyana irin wannan ra'ayi.
Ricardo ya ce:
"Wataƙila saurin da yake da shi a baya a wasanninsa ya ɗan ragu. Maimakon gudu na kilomita 200 a sa'a, yanzu yana gudu da kilomita 195 a sa'a. Har yanzu wannan sauri ne mai ban mamaki.
Matuƙar yana da kann ganiya, fasaha da ƙarfin tunani, zai ci gaba da kasancewa barazana ga abokan hamayya. Idan Ronaldo yana filin wasa, haɗari ne ga duk tawagar da zai fuskanta."
Tun bayan da Roberto Martinez ya karɓi ragamar horar da Portugal daga Belgium a shekarar 2023, Ronaldo ya buga wasa 31 cikin 39 da kocin ya jagoranta. Yawancin wasannin da bai buga ba sun kasance saboda rauni ko dakatarwa.
Abin lura shi ne, Portugal ta samu babbar nasararta a wannan lokaci ne a wasan da Ronaldo bai buga ba, lokacin da ta lallasa Luxembourg da ci 9-0 a watan Satumban 2023.
Haka kuma, nasara ta biyu mafi girma ita ce doke Armenia da ci 9-1 a Porto a watan Nuwamban bara, inda shi ma Ronaldo bai taka leda ba.
Bayan waɗannan wasanni biyu, muhawara ta sake ƙara ƙarfi kan ko Portugal na taka leda mafi ƙyau idan ƙyaftin ɗinta baya cikin fili.
Mai sharhi kan ƙwallon ƙafa a CNN Portugal, DAZN Portugal da gidan rediyon TSF, Sofia Oliveira, ta ce:
"A yanzu ba shi da irin ƙarfin wasan da zai sa ya kasance zaɓi na farko a tawagar da ke son lashe Kofin Duniya.
Abu ne mai sauƙi a ce Ronaldo bai kamata ya fara wasa ba a wannan gasar, kuma ni ma na yarda da hakan. Amma matsalar ita ce, tawagar Portugal ba fara shirin yaya za take wasa idan ta rabu da Ronlado ba,
Duk da cece-kuce da ake yi, abu ɗaya ya tabbata: yayin da Portugal ke shirin shiga Kofin Duniya na 2026, idanuwan duniya za su ci gaba da kasancewa kan Cristiano Ronaldo, wanda ke fatan kammala tarihinsa da wata babbar nasara a gasar da za ta kasance ta ƙarshe a rayuwarsa.
'Ba mu damu ba kan yadda za mu kasance a Portugal bayan Ronaldo ya yi ritaya'

Asalin hoton, Getty Images
Tafiyar da ɗan wasan ƙwallo kafa wanda ya yi fice a ƙasa baki ɗaya da duniya ba abu ne mai sauƙi ba.
Tsohon kocin Portugal, Fernando Santos, ya fi kowa sanin hakan.
Bayan da ya ajiye Cristiano Ronaldo a benci a Gasar Kofin Duniya ta 2022, Santos ya fuskanci suka mai tsanani a kafafen sada zumunta daga wasu magoya bayan Ronaldo, kuma daga baya ya bar mukaminsa.
A farkon wannan shekarar, an tambayi kocin Portugal na yanzu, Roberto Martinez, ko yana tsoron irin wannan martani idan ya sake yanke irin wannan hukunci a Kofin Duniya a 2026, amma ya nuna cewa bai damu da hakan ba.
Tasirin Ronaldo a Portugal ya kai matakin da shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Portugal (FPF), Pedro Proenca, ya kasance dole ya yi karin haske a wata hira da tashar SIC kan ko Ronaldo zai iya taka rawa wajen zaɓen sabon kocin Portugal idan Martinez ya bar aiki. Proenca ya musanta hakan gaba ɗaya.
Yayin da Ronaldo ke ci gaba da kasancewa cikin tawagar ƙasar, sanarwar da FPF ta fitar a watan Fabrairu kan haɗin gwiwa da kamfanin AVA CR7, wani kamfani na kula da lafiyar jiki mallakin Ronaldo, ta jawo cece-kuce a tsakanin masu bibiyar ƙwallon ƙafa.
Sai dai FPF ta ce babu wata matsala ko rashin gaskiya a wannan haɗin gwiwa.
A wata sanarwa da ta aikewa BBC Sport, hukumar ta ce:
"A mahangar FPF, wannan haɗin gwiwa ya dace da duk ƙa'idojin gudanarwa da suka dace kuma ba zai haifar da wata matsala ba dangane da matsayin Cristiano Ronaldo a matsayin kyaftin da ɗan wasan tawagar ƙasa.
Haka kuma, ya bayyana cewa Cristiano Ronaldo bai shiga tattaunawar yarjejeniyar ba, kuma ba shi ne abin da ake tattaunawa a kai ba. Dukkanin tattaunawar ta gudana ne kai tsaye tsakanin FPF da shugabannin kamfanin AVA."
A cikin watannin baya-bayan nan, yayin da tsohon ɗan wasan Manchester United da Real Madrid ke kara kusantar ƙarshen wasanninsa a gasar kofin duniya, ana ci gaba da tattaunawa kan yadda Portugal za ta rayu bayan ritayar Ronaldo.
A watan Mayu, FPF ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2026-27, inda take hasashen samun kuɗin shiga mafi yawa a tarihinta da suka kai Yuro miliyan 161, bayan kare shekara ta 13 a jere tana samun riba.
Da yake magana a wani taro kwanan nan, Pedro Proenca ya ce:
"FPF tana shirin wannan lokaci cikin natsuwa ba tare da tsoro ko tashin hankali ba. Cristiano zai kasance tare da tarihin Portugal har abada, ba kawai da FPF ba.
Mun san muhimmancin Cristiano sosai. Gaskiyar magana ita ce, sunan Cristiano Ronaldo da na FPF suna tafiya tare.
Amma abin da zan iya tabbatarwa shi ne cewa kuɗin shiga na hukumar suna da ƙarfi kuma za su ba mu damar ci gaba da gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata bayan lokacin da Cristiano zai yi ritaya."
Fiye da shekara 20 bayan da ya fara haskakawa a ƙwallon ƙafar Portugal, Ronaldo har yanzu yana tsakiyar al'amuran ƙwallon kafar ƙasar. Yanzu dai abin da ya rage masa shi ne wani ƙarin ƙoƙari na ƙarshe a Gasar Kofin Duniya ta 2026, wadda za ta iya zama ta ƙarshe a tarihinsa.











