Manchester United za ta tsawaita kwangilar Rashford, Bayern Munich ta tuntuɓi Zinedine Zidane

...

Asalin hoton, GETTY IMAGES

An wallafa

Da alama tsohon kocin Bayern Munich da Monaco da kuma Wolfsburg, Niko Kovac zai maye gurbin Jurgen Klopp a matsayin kocin Liverpool boss. (Mail)

Newcastle ta bayyana ɗan wasan tsakiyar Nottingham Forest kuma ɗan Birtaniya, Morgan Gibbs-White, mai shekara 24, a matsayin ɗan wasan da take matuƙar son ɗauka. (Mirror)

Liverpool za ta ɗauko ɗan wasan gefen Ingila, Marcus Edwards, mai shekara 25, daga Sporting Lisbon a kan £30m. (Football Insider)

Marcus Rashford ya shirya ci gaba da taka leda a Manchester United bayan Paris St-Germain ta bayyana cewa bata muradin ɗaukar ɗan wasan Ingilan mai shekara 26. (Sun)

Chelsea na shirin kai tayin ɗan wasan tsakiyar Netherland, Teun Koopmeiners, ɗan shekara 26, bayan wakilan ta sun je kallon wasan gasar Europa tsakanin Atalanta da Liverpool. (Sportmediaset - in Italian)

Tottenham na bibiyar ɗan wasan tsakiyar Leicester City kuma ɗan ƙasar Ingila, Kiernan Dewsbury-Hall kuma ɗan shekara 25 ɗin zai sanya hannu kan kwangilar £30m ko £40m a ƙarshen kakar bana. (Football Insider)

Haka nan kuma, Tottenham tana shirin ɗaukar ɗan wasan bayan Italiya ɗan shekara 21, Riccardo Calafiori, daga Bologna. (Tuttosport - in Italian)

Ɗan wasan gefen Sifaniya, Bryan Gil zai nemi raba gari da Tottenham, kuma Spurs ta shirya sallamar ɗan wasan mai shekara 23. (Give Me Sport)

Everton ta yi nisa da shirin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Belgium mai shekara 28, Leander Dendoncker wanda ke zaman aro a Napoli daga Aston Villa. (Football Insider)

Bayern Munich ta tuntuɓi Zinedine Zidane, wanda rabon sa da aikin horas da wata ƙungiya tun bayan barin Real Madrid shekara 3 baya, inda take neman maye gurbin Thomas Tuchel a bana (Marca - in Spanish)