Bayern Munich ta rasa Bundesliga a bana bayan lashe 11 a jere

Thomas Tuchel

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Bayern Leverkusen ta kwace kofin Bundesliga na bana a hannun Bayern Munich, wadda ta dauka 11 a jere mai 33 jimilla.

Ranar Asabar Bayern Munich ta doke FC Cologne da ci 2-0 a wasan mako na 29 a babbar gasar tamaula ta Jamus.

Bayern Leverkusen za ta buga wasa da Werder Bremen a gida ranar Lahadi, kuma da zarar ta yi nasara kennan ta lashe Bundesliga na farko a tarihi.

Idan har ba a doke Leverkusen ba a wasan za ta kafa tarihin buga karawa 29 a jere a Bundesliga ba tare da rashin nasara ba.

Kungiyar da Xabi Alonso ke jan ragama tana ta daya a teburi da maki 76 da tazarar maki 13 tsakani da Bayern Munich, bayan wasa 29 a kakar nan.

Alonso, wanda ya karbi kungiyar a bara tana cikin 'yan karshen teburi a Oktoban 2022, yanzu tana fatan lashe kofi uku a bana.

Tana sa ran lashe Bundesliga na farko a tarihi a kakar nan, sannan za ta buga wasan karshe a German Cup da Kaizerslauten.

Haka kuma Bayern Leverkusen, wadda ba a doke ta ba a bana ta yi nasara a kan West Ham 2-0 ranar Alhamis a wasan farko a Europa League zagayen quarter finals.

Harry Kane ne kan gaba a cin kwallaye a bana a Bundesliga mai 33, bayan wasa 29, amma ba zai daga kofin Bundesliga duk da yawan wadanda ya zura a raga.

Bayern mai Bundesliga 33 jimilla ta dauki 11 a jere tun daga 2011/12, lokacin da Borussia Dortmund ta lashe shi.

Kofi daya ne Bayern Munich ke fatan dauka a bana, shi ne Champions League, wadda za ta karbi bakuncin Arsenal a makon gobe a Jamus.

Arsenal da Bayern Munich sun tashi 2-2 a gasar zakarun Turai zagayen daf da ma kusa da na karshe ranar Talata 9 ga watan Afirilu.

Tuni dai kociyan Bayern Munich, Thomas Tuchel ya sanar cewar zai ajiye aikin horar da kungiyar da zarar an kammala wasannin bana.

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga:

  • Harry Kane Bayern Munich 32
  • Serhou Guirassy Stuttgart 25
  • Lois Openda RB Leipzig 22
  • Deniz Undav Stuttgart 16
  • Ermedin Demirovic Augsburg 15
  • Maximilian Beier Hoffenheim 13
  • Tim Kleindienst Heidenheim 1846 11
  • Niclas Fullkrug Borussia Dortmund 11
  • Donyell Malen Borussia Dortmund 11
  • Victor Boniface Bayer 04 Leverkusen 10
  • Omar Marmoush Eintracht Frankfurt 10
  • Jamal Musiala Bayern Munich 10