Real Madrid na son Alexander-Arnold, Alonso ya ƙi Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na kara nuna sha'awarta a kan dan bayan Liverpool da Ingila Alexander-Arnold, wanda kwantiraginsa a Anfield zai kare a shekara mai zuwa. (Relevo)
Kociyan Bayer Leverkusen Xabi Alonso zai tafi Bayern Munich maimakon Liverpool idan har zai koma wata kungiya a bazaran nan. (Sky Sports News)
Chelsea na kan gaba wajen zawarcin dan gaban Brazil Endrick amma kuma farashinsa ya sa Real Madrid ta yi galaba a kan kungiyar ta London wajen sayen matashin mai shekara 17 daga Palmeiras. (Telegraph )
A shirye Manchester United take ta kara nuna sha'awarta a kan dan bayan Brazil Gleison Bremer, mai shekara 27, wanda yarjejeniyar kwantiraginsa a Juventus ta tanadi sayar da shi a kan fam miliyan 43. (Mirror)
Maiyuwuwa Aston Villa ta sayar da dan wasanta na tsakiya na Ingila Jacob Ramsey, don gudun saba wa dokokin cinikayya na sayen 'yan wasa. (Football Insider)
Sir Jim Ratcliffe yana son sauya aikin manajan kungiya a Manchester United, saboda ya fi dacewa da aikin babban mai horarwa, wanda aikinsa kusan shi ne na atisaye. (Telegraph)
Sai dai kuma manajan na yanzu Erik ten Hag zai iya barin kungiyar idan har ba zai yarda da sauyin aikin nasa ba. (Star)
Kila Newcastle United ta sayar da mai kai hari Alexander Isak, na Sweden a bazara domin kiyayewa da ka'idojin cinikin 'yanwasa, kuma kila ya tafi Arsenal wadda ta dade tana sha'awarsa. (Football Insider)
Dan wasan gaba na gefe na Sunderland Jack Clarke, ba zai kulla sabuwar yarjejeniya ba a kungiyar ta gasar kasada Premier wato Championship, wanda hakan zai iya sa West Ham da Lazio su sake kunno kai wajen zawarcinsa. (The i)
Watakila tsohon babban mai daukar wa Arsenal sababbin 'yan wasa Sven Mislintatya tafi Borussia Dortmund a matsayindarektan wasanni na kungiyar. (Sky Sports )












