'Liverpool da Bayern na son naɗa Alonso a matsayin koci'

Alonso

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shugaban ƙungiyar Bayern Munich na jeka na yika Uli Hoeness ya ce ƙungiyarsa da Liverpool na hammaya da juna domin naɗa Xabi Alonso a matsayin manaja.

Alonso ya murza leda a ƙungiyoyin biyu kuma yana kan hanyarsa ta jagorantar Bayer Leverkusen domin lashe kofin gasar Bundesliga a karon farko a tarihin ƙungiyar.

Bayern da Liverpool na neman wanda za su bai wa kocin ƙungiyoyinsu a bazarar bana.

"Kungiyoyi kamar Liverpool Real Madrid, Leverkusen da FC Bayern, suna aiki a kansa," in ji Hoeness.

"Ya nuna cewa shi babban kocin ne. Akwai matukar wuya samun kocin da bai da aiki."

Thomas Tuchel zai bar Bayern Munich a ƙarshen kakar wasa ta bana a yayin da Jurgen Klopp ya sanar da cewa zai bar Liverpool.

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya sabunta yarjejeniyarsa har zuwa shekara ta 2026.

Alonso ya shafe shekaru biyar a matsayin ɗan wasan Real bayan ya bar Liverpool sannan daga Real ya tafi Bayern.

Yarjejeniyar Alonso a Leverkusen za ta kare ne a 2026.