‘Yan Najeriyar da ambaliyar ruwa ta lalatawa katunan zabe sun koka da rashin samun damar zaben 2023

Katunan zabe

Asalin hoton, Other

An wallafa

Cikin masu wannan koke har da wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ta lalatawa dukiyoyi da sauran mahimman takardu har ma da katunan zabensu.

Idan ba a manta ba an samu mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a damunar 2022, abin da ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan Najeriya.

Ambaliyar ruwan ta yi sanadin lalacewar dukiyoyi har ma da katunan zabe.

Katin zaben dai da shi ne ‘yan Najeriya za su iya zaben mutanen da suke so su shugabance su wala a matakin gwamnatin tarayya da ta jiha da kuma kananan hukumomi a babban zaben da ke tafe.

To amma da dama daga cikin ‘yan Najeriyar sun ce zaben 2023 fa sai dai su zuba ido.

Malam Adamu Jibril, da ke zaune a kauyen Kumsa a karamar hukumar Birniwa da ke jihar Jigawa a arewacin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa idan ya tuna bashi da katin zabe sai takaici ya kama shi.

Ya ce, "Katina ya bata a sanadiyyar ambaliyar ruwa, don haka ji nake kamar gwamnatin da nake hari na zaba ba za ta samu sa’a ba.”

Shi kuma wani mutum da BBC ta zanta da shi wanda gobara ta yi sanadin lalacewar katin zabensa, ya ce akwai muhimman takardunsa da suka kone sakamakon iftila’in gobarar da ya fuskanta a gidansa kuma ciki har da katin zabensa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce, "Baka ji irin haushin rashin katin zaben da nake ji ba, na yi kokari na samu wani amma abin ya ci tura saboda ban san lokacin da Hukumar Zabe ta yi wa masu matsala irin tawa wani katin ba, don haka tun da ba zan samu damar yin zaben 2023 ba, ina fatan Allah ya zaba mana shugabanni na gari masu jin kan talaka.”

Ita ma wata mata da ke garin Jambawa a karamar hukumar Ringim da ke jihar ta Jigawa, ta shaida wa BBC cewa, katunan zabenta da na mijinta duk sun bata sakamakon ambaliyar ruwan da suka fuskanta.

Ta ce, "Takardunmu ni da mijina duk sun bi ruwa, don haka idan na tuna bani da katin zabe sai inji ban ji dadi ba, zuciyata ta kan yi ciwo ganin bani da damar kada kuri’a a zaben 2023.”

Koda BBC ta tuntubi hukumar zaben kasar a kan makomar irin wadannan mutanen da suka rasa katunan zabensu, ta ce bakin alkalami ya riga ya bushe.

Wata jami’a a hukumar da BBC ta tuntuba, Hajiya Zainab Aminu Abubakar, ta ce ya kamata wadanda suka rasa katunan zabensu a dalilin ambaliyar ruwa ko gobara, sun kai kukansu a lokacin da aka bude dama na yin rijistar katunan zabe a baya don a sake yi musu sabon kati, to amma a yanzu a lokacin da ake dab da zaben wannan damar ta wuce, sai kuma bayan an kammala zabe.