Yadda batun raba katin zabe ke jan hankalin ‘yan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Soma ba da katunan zaɓe na din-din-din ga wasu daga cikin masu zaɓe a Najeriya ya ja hankalin 'yan kasa inda kowa ke bayyana ko tofa albarkacin bakinsa.
A wannan Litinin din Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Inec ta soma wannan aiki kuma mutanen da za a bai wa katunan su ne mutanen da suka ba da sunayensu daga farkon 2022, zuwa lokacin da aka rufe aikin a watan Yuli.
Sai dai kuma duk da irin tsare-tsare da Inec ta ce ta yi, ana ta samun masu korafi da kokawa kan dogayen layuka wajen samun katin, da kuma wadanda suka hau shafukan sada zumunta musamman Tuwita da nasu ƙorafin.
Za dai a shafe kwanaki ana wannan aiki na raba katunan zabe a matakin ƙaramar hukuma kafin a koma matakin mazaɓu.
Yaya rabon ke kasancewa?

Asalin hoton, Getty Images
Ana raba katunan ne a ofisoshin INEC na kananan hukumomi kawo yanzu, inda jama'a ke bin layi a mazaɓu.
Duk mutumin da ya zo karbar katin sai ya gabatar da shaidar cewa ya yi rijista a baya sannan sai a duba sunansa a kundin rijistar zaɓe sai kuma a duba masa katin.
Idan an sami katin sai kuma a rubuta sunansa ya saka hannu cewa ya karbar.
Amma da farko sai mutum ya duba sunansa a kundin rijistar da aka yi baje-kolinta a jikin bango.
Wadanda ba su ga sunayensu ba a kan ba su wata takarda su cike sannan sai a bukaci su dawo daga baya don karbar katinsu.
Sai dai wasu rahotanni na cewa ana samun dogayen layuka wajen karbar kati, sannan akwai wadanda ba su samu katinsu ba saboda wasu dalilai.
Me mutane ke cewa a shafukan sada zumunta?
Galibi dai abin da ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta na Alla-wadai da kazamin harin da aka kai wa ofishin Inec da ke Imo.
Mutane dai na ganin akwai bukatar gwamnati ta yi da gaske domin inganta tsaro ganin yanayin abubuwan da ke faruwa a Najeriya.
Sannan akwai masu fitowa dauke da katunansu suna nuna cewa su nasu katin zaben ya shiga hannu, duk da cewa wasun su na ƙorafin shan wahala kafin karbar katin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
@HiikyaaTor ya ce: A ranar da INEC ta soma raba katunan zabe, 'yan daba da bata-gari suka far wa ofishin INEC a jihar Imo-Owerri. Akwai ayar tambaya anan!!! Wane ne makiyin dimokuradiya? Me ya sa abubuwan nan ke faruwa a Kudu maso gabashi? Ya Ubangiji, ka tona asiri..
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
@fopara03 ya ce: Yanzu nan na karbi nawa katin zaben sannunku da kokari Inec. Don Allah ku je ku karbi naku katin
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3

Karshen labarin da aka sa a X, 4
@D_goodybag ta ce; Ga abubuwan da nake gani anan. Tsarin akwai gajiyarwa, dandazon jama'a ya yi yawa. Inec su inganta tsarin
Sannan abu na uku da ake tattaunawa a kai shi ne yadda a wasu ofisoshin jami'an Inec din katunan ba su samu ba sai iske jami'an hukumar na ta hidimominsu.
Akwai kuma masu karfafawa matasa su fita su karbi katinsu domin shi ne yancinsu wajen zaben mutumin da zai raya kasa.
Inec Ta ce za a raba katunan ne daga ranar 12 ga watan Disambar 2022 zuwa 22 ga watan Janairun 2023, kuma za a yi rabon ne a dukkan kananan hukumomin Najeriya 774.
Daga ranar 15 zuwa 22 ga watan na Janairu, za a sake komawa ofisoshin hukumar zaben da ke jihohi domin ci gaba da raba katunan.