Shin tsaro ya inganta a mulkin Buhari?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ahmad Tijjani Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
Yayin da wa'adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na biyu ke zuwa ƙarshe, wani batu da ake ci gaba da tafka muhawara a kai, shi ne batun tsaro cikin ƴan shekarun baya-bayan nan a ƙasar.
A hirarsa da gidan talbijin na Channels ranar Litinin, mai magana da yawun shugaban mai barin gado, Femi Adesina ya ce Muhammadu Buhari zai bar Najeriya, cikin aminci da gagarumin ci gaban tsaro, a kan yadda ya same ta farkon mulkinsa.
Kalaman Femi Adesinan dai sun janyo ka-ce-na-ce a tsakanin al'ummar ƙasar, ciki har da masana harkokin tsaro, inda ake ci gaba da tsokaci.
Wasu masana kamar Dakta Kabiru Adamu na da ra'ayin cewa Shugaba Buhari ya yi ƙoƙari a fannin tsaro, musamman ma zimmar da ya nuna a wa'adin mulkinsa na biyu da ke gab da ƙarewa.
Mai sharhin kan harkokin tsaro a yankin Sahel ya ce Buhari ya kuma yi ƙoƙari wajen taimaka wa hukumomin tsaron Najeriya ta hanyar sayo sabbin kayan aikin sojoji da inganta horas da dakarun tsaro.

Asalin hoton, Linkedin/Kabir Adamu
Ya ce a ƙarƙashin gwamnatin Buhari, Najeriya ta yi bitar yawancin dokokin da suka kafa hukumomin tsaronta.
An dai ɗauki tsawon lokaci ba a yi irin wannan hoɓɓasa ba, musamman dokar da ta kafa rundunar ƴan sandan ƙasar, wadda rabon da a yi mata bita tun zamanin mulkin mallaka.
A cewarsa, kafa hukumar taƙaita bazuwar makamai da bindigogi da Shugaba Buhari ya yi, shi ma muhimmin abu ne da ya taimaka matuƙa a fannin tsaro.
A nasa ɓangare, Audu Bulama Bukarti, wanda babban mai bincike kan harkokin 'yan ta-da-ƙayar-baya a Afirka ne, ya ce idan aka duba wani sashe, za a iya cewa tsaro ya inganta a ƙarƙashin mulkin Buhari.
"Amma idan ka duba ƙasar gaba-ɗaya, za ka ga al'amura sun ƙara rurucewa a mulkin Buhari.
Saboda yawan mutanen da ake kashewa ya ƙaru, yawan ƙungiyoyi masu riƙe da makamai ya ƙaru, da kuma wuraren da ake kai wa hare-hare," in ji Bukarti.
Ya ce idan aka ɗauki ɓangaren rikicin Boko Haram, za a ga cewa al'amura sun inganta a zamanin Muhammadu Buhari musamman arewa maso gabas.
"Lokacin da Buhari ya zama shugaban ƙasa bama-bamai na tashi a kusan ko'ina.
Ana fuskantar munanan hare-hare a Kano da Kaduna da Abuja da wurare daban-daban na arewacin Najeriya.

Amma bayan hawansa, an yi nasarar daƙile rikicin Boko Haram," in ji Barista Bukarti.
Ya ce duk da yake, barazanar Boko Haram ta ragu, amma har yanzu suna kai hare-hare da kashe mutane a ƙauyuka.
Haka kuma ana iya cewa matsalar tsaron ta yaɗu daga arewa maso gabas, zuwa wasu wurare na arewa ta tsakiya da arewa maso yamma, yankunan da kafin zuwan Buhari, babu irin wannan matsala ta yanzu.
Ya ci gaba da cewa a lokacin mulkin Buhari ne, matsalar ƴan fashin daji ta ƙara ƙamari, duk da yake akwai su a baya, amma ba su da ƙarfin kai hari a kan makarantu da gidajen yari da kuma sansanonin sojoji.
"A ƙarƙashin shugabancin Buhari ne muka ga ana sace dubban mutane duk shekara, sannan a lokacinsa ne kuma ƙungiyar IPOB ta ɗauki maƙamai, ga kuma kashe-kashen ƴan arewa mazauna yankin, da far wa ofisoshin INEC," in ji Bukarti.
An samu raguwar kashe-kashe?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Game da kashe-kashen ƴan Najeriyan da ake ci gaba da samu, Dakta Kabiru Adamu, ya ce a shekarar 2014 - 2015 lokacin da shugaba Buhari ya karɓi mulki, an samu kashe-kashe mutane kusan 13,000.
Kuma a lokacin ne, Boko Haram ta bayyana a matsayin ƙungiyar da ta fi aikata munanan kashe-kashe a duniya.
Amma ya ce bayan zuwan Buhari, an samu raguwar kashe-kashen zuwa 6,000 ko 5,000 ko kuma 7,000.
Sai dai, ya ce ana cikin haka ne, sai aka samu canjin hare-haren ta'addancin da ake aikatawa.
Daga bisani, an koma kai hare-hare ne zuwa arewa maso tsakiyar Najeriya da kuma arewa maso yamma musamman jihohin Kaduna da Zamfara da Neja da Kogi har ma da Ondo da sauransu.
"Ayyukan ƴan bindiga sun ƙaru a lokacin Buhari fiye da kafin hawansa karagar mulki, inda aka samu mace-macen mutane kimanin 11,000 a shekarar 2022.
Wannan ne ya sa akwai ayar tambaya a kan iƙirarin da Femi Adesina ke yi," in ji Dakta Kabiru Adamu.
Ya ce bai dace Adesina ya yi irin wannan iƙirari a wannan lokaci ba.
Ko da yake, in ji shi gwamnati ta yi hobɓasa, amma akwai kura-kurai da suka kamata a zauna, a yi duba kansu da nufin kawo gyara.
Shi ma Barrister Bulama Bukarti, ya ce alƙaluma sun nuna cewa a shekara bakwai na mulkin Buhari, daga watan Maris ɗin 2015 zuwa Maris 2022, ƙungiyoyin ƴan ta'adda sun kashe ƴan Najeriya 55,430.
Ya ce ko lokacin mulkin Goodluck Jonathan, ba a kashe ƴan Najeriya masu yawa kamar a zamanin Buhari ba.
A cewarsa, bisa ƙididdiga a ƙalla yanzu ana kashe mutum 7, 918 duk shekara a Najeriya.
Rashin shingen bincike ma nasara ce?
Femi Adesina dai a tattaunawarsa da Channels TV ya yi iƙirarin cewa kafin zuwan gwamnatinsu, akwai shingayen bincike a yawancin sassan arewacin Najeriya, lamarin da ya ce ko janye su ma, wata manuniyar nasara ce da aka samu.
Sai dai, Barista Audu Bulama Bukarti ya ce abin da ya sa yanzu babu shingayen bincike shi ne saboda yaƙin da Najeriya ke yi da ta'addanci ya sauya salo.
Ya ce abin da ya sa ake da shingayen tsaro a hanyar Abuja zuwa Kano da hanyar zuwa Maiduguri da kuma Gashua, shi ne Boko Haram a lokacin ta matsa da kai hare-haren bam a cikin garuruwa.
"Yanzu kuma hare-haren sun fi karkata ne kan ƙauyuka musamman a jihohin Zamfara da Kebbi da Sokoto da Kaduna da kuma a yankin arewa maso gabas," cewar Bukarti.
"Ba wai babu barazanar tsaro ba ne a halin yanzu, amma salon faɗan ne ya canza."
Koma-bayan tattalin arziƙi
Batun taɓarɓarewar tsaro, ya haddasa wa Najeriya gagarumar koma-baya ta fuskar tattalin arziƙi da ci gaban ƙasa.
Matsalar kuma ta haifar da ɗumbin matsaloli ga 'yan ƙasar.
Dubban ɗaruruwan 'yan Najeriya ne suka tsere daga gidajensu zuwa gudun hijira a jihohi kamar Borno da Yobe da Adamawa da Zamfara da Katsina da kuma Neja.
An rufe makarantu masu yawa bayan ƴan ta-da-ƙayar-baya da 'yan fashin daji sun ƙaddamar da munanan hare-hare da sace ɗaruruwan ɗalibai don neman kuɗin fansa.
Ɓangaren tattalin arziƙi na daga cikin mafi shan wuya sanadin hare-haren ta'addanci.
Hukumomi sun riƙa rufe kasuwanni saboda hare-haren da Boko Haram ta riƙa kai wa a arewa maso gabas.
A arewa maso yamma kuwa, ayyukan 'yan fashin daji sun janyo rufe kasuwanni don hana musayar kayan sata da sace kayan abinci da na masarufi da kuma uwa-uba mutanen gari.











