Hotunan Afirka na mako daga 24 zuwa 30 ga watan Yunin 2022

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga sassan nahiyar Afirka da kewaye na 'yan nahiyar a wannan makon:

Wasu mawaka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mawakan gargajiya suna raye-raye a yayin da ake bikin tarbar hakorin tsohon firaiministan Kongo Patrice Lumumba - ranar Lahadi a garin Shilatembo, inda aka yi masa kisan-gilla a 1961...
Mawaka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kazalika kungiyar mawaka ta cashe a Lumumba a wajen bikin nuna girmamawa ga tsohon firaiministan a yayin da ake zagayawa da akwatin gawarsa gabanin jana'izarsa ranar Alhamis.
Mata a Accra, babban birnin kasar Ghana, sun shiga jerin zanga-zangar da aka yi ta kwana biyu ranar Laraba, domin jawo hankalin gwamnati game da yanayin tsadar rayuwar da ake fama da shi...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mata a Accra, babban birnin kasar Ghana, sun shiga jerin zanga-zangar da aka yi ta kwana biyu ranar Laraba, domin jawo hankalin gwamnati game da yanayin tsadar rayuwar da ake fama da shi...
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba wadda ita ce ranar farko ta zanga-zangar, lamura sun kazance lokacin da 'yan sanda suka fito domin kare wasu manyan 'yan siyasa, cikinsu har da Mataimakiyar Ministan Kudi Abena Osei Asare (wadda ke tsakiya).
A babban birnin kasar Sudan, Khartoum, mutane sun yi zanga-zanga ranar Alhamis domin tilasta wa sojoji su mika mulki a hannun farar-hula.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A babban birnin kasar Sudan, Khartoum, mutane sun yi zanga-zanga ranar Alhamis domin tilasta wa sojoji su mika mulki a hannun farar-hula.
Shugabannin kungiyar kasashe renon Ingila, da suka hada da Firaiministan Birtaniya Boris Johnson, sun samu tarba ta musamman daga wurin mawaka da makada a Kigali, babban birnin  Rwanda's capital, Kigali, ranar Juma'a da maraice

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugabannin kungiyar kasashe renon Ingila, da suka hada da Firaiministan Birtaniya Boris Johnson, sun samu tarba ta musamman daga wurin mawaka da makada a Kigali, babban birnin Rwanda's capital, Kigali, ranar Juma'a da maraice
Wata manomiya a Ethiopia yayin da ta cire amfanin gonarta ranar Juma'a a kauyen vineyard mai nisan kilomita 110 kudu maso gabashin Addis Ababa...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata manomiya a Ethiopia yayin da ta cire amfanin gonarta ranar Juma'a a kauyen vineyard mai nisan kilomita 110 kudu maso gabashin Addis Ababa...
Ma'aikaciyar gidan sayar da barasa na Awash Wine tana sansanawa da kuma dandana giyar da aka yi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ma'aikaciyar gidan sayar da barasa na Awash Wine tana sansanawa da kuma dandana giyar da aka yi.
Wani mai sana'ar daukar hoto ya dauki hoton wannan dan ci-ranin dan kasar  Sudan ranar Asabar bayan ya isa yankin Melilla da ke karkashin ikon Sifaniya duk da dukan da jami'an tsaro suka yi masa...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai sana'ar daukar hoto ya dauki hoton wannan dan ci-ranin dan kasar Sudan ranar Asabar bayan ya isa yankin Melilla da ke karkashin ikon Sifaniya duk da dukan da jami'an tsaro suka yi masa...
Akalla mutum 23 sun mutu a wani rikici a yayin da suka yi yunkurin tsallakawa daga Morocco kuma ranar Talata, a babban birnin kasar, Rabat, 'yan ci-rani sun yi zanga-zanga inda suka yi kira a gudanar da bincike kan batun.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Akalla mutum 23 sun mutu a wani rikici a yayin da suka yi yunkurin tsallakawa daga Morocco kuma ranar Talata, a babban birnin kasar, Rabat, 'yan ci-rani sun yi zanga-zanga inda suka yi kira a gudanar da bincike kan batun.
Wata mata da 'ya'yanta uku a kan babur a birnin Sikasso na kasar ranar Asabar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata da 'ya'yanta uku a kan babur a birnin Sikasso na kasar ranar Asabar.
Algeria tana karbar bakuncin wasannin yankin tekun Bahar Rum, wanda ake gudanarwa bayan kowace shekaru hudu, kuma a gasar cin lambar zinare ta kareti ta mata masu nauyin kilogiram 50 , 'yar kasar Masar Salama Reem (ta hagu) ta fafata da 'yar kasar Algeria Cylia Ouikene. Ouikene ce ta yi nasara.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Algeria tana karbar bakuncin wasannin yankin tekun Bahar Rum, wanda ake gudanarwa bayan kowace shekaru hudu, kuma a gasar cin lambar zinare ta kareti ta mata masu nauyin kilogiram 50 , 'yar kasar Masar Salama Reem (ta hagu) ta fafata da 'yar kasar Algeria Cylia Ouikene. Ouikene ce ta yi nasara.
Wata mota da ta shiga gasar tseren motoci ta Safari a Kenya ta tayar da kura a kudancin Kogin Naivasha ranar Lahadi, ranar da aka rufe gasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mota da ta shiga gasar tseren motoci ta Safari a Kenya ta tayar da kura a kudancin Kogin Naivasha ranar Lahadi, ranar da aka rufe gasar.