Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayern na zawarcin Robertson, Madrid za ta ɗauko ƙanin Mbappe
Bayern Munich na zawarcin dan wasan baya ta gefen hagu na Liverpool da Scotland Andy Robertson dan shekara 29, domin maye gurbin dan wasan Kanada Alphonso Davies, wanda ke shirin komawa Real Madrid. (Daily Mail)
Damuwar da Arsenal ta nuna a kan raunin da dan wasa mai kai hari na kasar Brazil Gabriel Jesus ke fama da shi , ta na cikin dalilan da su ka sa ta ke neman wani dan wasa mai kai hari inda a ciki akwai dan wasan Brentford , Ivan Toney, da Victor Osimhen na Napoli, da Joshua Zirkzee na Bologna da kuma Viktor Gyokeres na Sporting. (Daily Mail)
Kungiyar ta Asenal ta na kuma son daukar mai tsaron bayan Ajax Jorrel Hato dan shekara 17 , sai dai ita ma Ajax na son ya ci gaba da taka leda a kulob din (Evening Standard)
A wani bangare na yarjejeniyar siyan Kylian Mbappe, mai shekara 25, Real Madrid ta amince ta dauko kanin dan wasan gaban Faransa, Ethan dan shekara 17 daga Paris St-Germain. (OK Diario - in Spanish)
Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane, mai shekara 51, na cikin jerin sunnayen wadanda ake ganin Sir Jim Ratcliffe zai zaba domin maye gurbin Erik ten Hag a matsayin kocin Manchester United. (Foot Mercato - in French)
Kocin Brighton Roberto de Zerbi shi ma ya na cikin wadanda ake ganin za su maye gurnin dan kasar Netherlands. (MEN)
Bayern Munich ta na sha’awar kocin Seagulls De Zerbi inda kocin Bayer Leverkuse Xabi Alonso da tsohon kocin Jamus Hansi Flick na cikin wadanda zsa su maye gurbin kocinta. (Sky Germany)
Aikin Vincent Kompany ba ya fuskantar barazana a Burnley, duk da cewa kungiyarsa na neman komawa gasar Championship. (The Athletic)
Barcelona na tunanin dauko tsohon mai tsaron gidan Manchester United David de Gea,mai shekara 33, yayin da a yanzu dan kasar Sfaniya ba shi da wata kungiya da zai yi wa wasa. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Newcastle United da Tottenham na zawarcin dan wasa mai hari na Eintracht Frankfurt da Masar Omar Marmoush, dan shekara 25 wanda ya zira kwallaye 10 a wasanni 18 da ya buga a gasar Bundesliga ta bana . (Bild via Shields Gazette)
Liverpool na son ta dauko dan wasa tsakiya na Porto da Argentina Alan Varela, dan shekara 22. (Mirror)
Barcelona na son ta maye gurbin Xavi, wanda zai tafi a karshen kakar wasanni da kocin Inter Milan Simone Inzaghi. (Mundo Deportivo - in Spanish)